Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakatar Da ‘Yar Wasan Tseren Najeriya Blessing Okagbare A Gasar Olympics 


'Yar wassen tseren Najeriya Blessing Okagbare a tsakiya
'Yar wassen tseren Najeriya Blessing Okagbare a tsakiya

Sai dai kamar yadda doka ta tanada, Okagbare na dama ta nemi a sake yin gwaji a karo na biyu don a tabbatar da sahihancin sakamkon farko.

Hukumar AIU da ke sa ido kan ‘yan wasan tsere, ta dakatar da ‘yar wasan Najeriya Blessing Okagbare bayan da aka gano burbushin kwaya da ke kara kuzuri da gina jiki a jikinta.

Dakatar da Okagbare na zuwa ne sa’o’i gabanin ta kara a matakin semi-final na tseren mita 100 a zangon mata a gasar ta Olympics a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

“An samu alamun kwayar da ke kara gina jiki a jikin Okagbare a wani gwaji da aka mata a ranar 19 ga watan Yuli gabanin a bude gasar.” Hukumar ta AIU ta ce kamar yadda AP ya ruwaito.

Sai a ranar Juma’a ne aka samu sakamakon gwajin bayan da Okagbare ta riga ta kara a tseren mita 100 a ranar da aka bude wasannin tsere a birnin Tokyo a cewar AIU.

‘Yar wasan tseren ta Najeriya ta riga ta lashe wani wasa cikin dakikoki 11.5 tana kuma shirin karawa a matakin semi-finals a ranar Asabar.

Da safiyar ranar Asabar hukumar ta AIU ta sanar da Okagbare inda ta ce ba za ta kara a wasan gaba, hakan kuma na nufin mai yiwuwa ta fice kenan a gasar baki daya.

Sai dai kamar yadda doka ta tanada, Okagbare na dama ta nemi a sake yin gwaji a karo na biyu don a tabbatar da sahihancin sakamkon farko.

‘Yar shekara 32, Okagbare ta taba lashe azurfa a wasan tsalle mai dogon a gasar Olympics ta 2008 a Beijing da kuma gasar zakaru ta 2013.

Ta kuma taba lashe tagulla a tseren mita 200 a gasar kasa da kasa da aka yi a Moscow a shekarar 2013.

Matakin dakatar da Okagbare na zuwa ne kwana uku bayan da hukumar ta AIU ta sallami wasu 'yan wasan Najeriya 10 cikin 'yan wasan 20 da aka kora daga kasashe daban-daban a gasar ta Olympics saboda sun fadi a gwajin da aka masu wanda ke duba ko suna dauke da burbushin wata kwaya mai sa kuzari.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG