Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Guda Ya Rasa Ransa A Wata Hatsaniya Da Ta Biyo Bayan Rusa Coci A Borno 


Gwamnan Borno Babagana Zulum
Gwamnan Borno Babagana Zulum

Baya ga mutum daya da ya mutu wasu mutum biyar sun jikkata wadanda aka kai su asibiti don samun kulawa.

Akalla mutum daya ne ya rasa ransa bayan wata hatsaniya da ta biyo bayan rusa wata Coci da jami’an da ke kula da tsara birnin Maiduguri BOGIS na jihar Borno suka yi a ayyukan rusau da suke yi.

Har ila yau wasu mutane biyar sun jikkata a rikicin.

Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito sunan matashin da ya rasu a matsayin Ezekiel.

Lamarin ya faru ne a lokacin da matasa suka yi boren nuna adawa da aikin rusa Cocin EYN wacce hukumar ta BOGIS ta saka cikin jerin wadanda za a rusa domin a cewarta an gina ba bisa ka’ida ba.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro da ke rakiyar jami’an hukumar da ke rusa wuraren sun bude wuta akan masu zanga-zangar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar matashi da jikkata mutum biyar.

Wata sanarwa da kakakin gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum Malam Isa Gusau ya fitar, ta tabbatar da aukuwar lamarin ta kuma yi Allah wadai da bude wutar da jami’an suka yi akan masu boren.

Sannan sanarwar har ila yau ta yi tir da matasan da suka rika jifan jami’an tsaron da duwatsu.

Gwamna Zulum ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma shugabannin Cocin.

Ya kuma kira shugaban kungiyar Kiristocin jihar Borno ta CAN, Bishop Mohammad Naga ta wayar tarho, inda ya jajinta masa kan wannan al’amari.

Sanarwar ta kara da cewa gwamna Zulum ya ba mataimakinsa Umar Kadafur umarnin ya kai wa wadanda ke kwance a asibiti ziyara tare da biyan dukkan kudaden jinyar da za a caje su.

Gwamna Zulum ya kuma ba rundunar ‘yan sanda jihar umarnin su gudanar da binciken gaggawa kan musabbabin wannan hatsaniya.

Sanarwar ta kuma kara da cewa "hukumar ta BOGIS ta rusa masallatai da Coci-coci da dama da aka gina ba bisa ka’ida ba a birnin na Maiduguri a wani mataki na sake fasalin birnin."

XS
SM
MD
LG