Bankin na CBN ya kuma ce zai dakatar da ayyukan ba da lasisi ga masu neman bude kasuwancin canjin kudaden kasashen waje.
Fadar shugaban kasar ta ce cikin mako na biyu na watan Agusta shugaba Buhari zai koma Najeriya.
Shugaban kungiyar Kiristoci ta jihar Kaduna, Rev. Joseph John Hayeph ya ce babu hannun gwamnati a kokarin karbo wadannan dalibai.
Tawagar ‘yan wasan kwallon kafar Faransa a gasar wasannin Olympics da ake yi Tokyo na kasar Japan, ta lallasa abokiyar hamayyarta ta Afirka ta Kudu da ci 4-3.
Sai dai babu bayanai da ke nuna cewa kudin fansa aka biya aka sako wannan tawagar daliban ko akasin haka.
"Kuma muna gode maku domin kun taka rawar gani. Babu shakka wannan Muqabala wacce aka shirya, Malamai sun yi aikin nasu na malanta."
Wata kotun tarayya a Najeriya, ta samu wasu masu fashin teku su goma da laifin satar wani jirgin ruwan ‘yan kasuwa mai suna FV HAILUFENG II inda ta yanke masu hukuncin shekara 12 a gidan yari.
A shekarar da ta gabata aka tura sojojin kasar zuwa Amurka don samun horo kan yadda za su sarrafa jiragen.
"Za ka ga mutanen da ke zaune tare, yarensu daya, addininsu daya amma suna kashe kansu tare da sace-sacen shanu.” In ji Buhari.
A farkon watan Mayu shugaba Muhamnmadu Buhari ya dakatar da Bala Usman don a samu damar gudanar da bincike kan zargin da ake mata.
A ranar 8 ga watan Yuli, ‘yan bindiga suka far wa makarantar wacce ke karamar hukumar Chikun, suka yi awon gaba da dalibai sama da 100.
“Sun sha matukar wahala. Bai dace yadda aka rika zaginsu a shafukan intanet ba. Na san akwai zafi ka ga tawagarku ta sha kaye, amma bai dace a ce ana zaginsu ba."
A ranar 17 ga watan Yuni, ‘yan bindiga suka far wa makarantar sakandaren ta Yauri suka sace dalibai da dama da wasu malamansu.
Bayan da ya duro daga jirgin, Dairo ya yi amfani ne da duhun dare ya yi ta kaucewa tungar maharan da ke cikin dajin har ya kai sansanin sojoji, inda daga karshe aka cece shi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da fadar shugaban kasar da fitaccen malamin addinin suke kai ruwa rana ba, ko a watan Afrilu, sun yi ka-ce-na-ce bayan da Bishop Kukah ya yi tsokaci kan yadda matsalar tsaro take kara ta’azzara a Najeriya.
Akwai rahotanni da ke cewa, abokanan wasan Kane sun ce mai yi wa dan wasan ba zai koma kungiyar ta Tottenham a kakar wasa mai zuwa, saboda ana alakanta shi da tafiya kungiyar Man City.
A ranar 8 ga watan Yuli cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta sanar da bullar sabuwar cutar ta COVID-19 nau’in Delta, wacce masana suka ce tana da saurin yaduwa.
A ranar Juma’a 16 ga watan Yuli aka gurfanar da Abduljabbar a gaban wata babbar kotun Shari’a da ke Kofar Kudu wacce ke karkashin jagoranci Alkali Ibrahim Sarki Yola.
Hakan na nufin idan an kammala aikin, za a samu hanyar sufurin jirgin kasa tun daga Abuja har zuwa Kano.
Janar Ahmed na kan hanyar komawa Abuja ne daga Okene a lokacin da maharan suka budewa motarsu wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Domin Kari