A ranar Juma’a an ga Basij-Rasikh tana kona takardun da ke dauke da bayanan daliban makarantar gudun kada ‘yan kungiyar Taliban su binciko su daga baya.
A lokacin da yake murza leda a United, a tsakanin 2003 zuwa 2009, Ronaldo wanda dan asalin kasar Portugal ne ya zura kwallaye 118 a wasannin 292.
Hakan ya biyo bayan tayi da Manchester City ta yi masa a ranar Laraba na kwantiragin shekara biyu akan kudi euro miliyan 15.
“Rahoton ya kunshi duk binciken da aka yi kan lamarin, hujjoji, da kuma bahasin da DCP Abba Kyari ya bayar da na sauran mutanen da lamarin ya shafa.” Sanarwar ta ce.
Wannan shi ne karon farko cikin shekara 44 da kamfanin NNPC ya bayyana baki dayan ribar da ya samu tun da aka kafa shi in ji sanarwar Femi Adesina.
Dalibai kusan 100 ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su ciki har da kananan yara ‘yan kasa da shekara 7, lamarin da ya janyo kakkausar suka a ciki da wajen Najeriya.
Kwantiragin Cristiano Ronaldo a Juventus da ke gasar Serie A a Italiya zai kare ne a watan Yunin 2022 amma yana da damar da zai iya tafiya idan yana so kafin a rufe kasuwar sayar da 'yan wasa.
“Matsayar gwamnati ita ce, kada kowa ya biya kudin fansa don ceto ‘ya’yansa, na san wannan abu mai wuya ne ga iyaye, amma a karshe idan aka biya, hakan zai rika mayar da hannun agogo baya.” In ji Mohammed.
“Wannan danyen aiki zai zaburar da dakarunmu wajen kawar da duk wasu muggan ayyuka, wanda sojojinmu suka kuduri aniyar aiwatarwa nan ba da jimawa ba.”
Mbappe ya ci wa PSG kwallaye 133 ya kuma taimaka aka ci wasu 63 a wasanni 174 da ya buga a zamansa a kungiyar.
“Me ye naku na shiga ku yi kane-kane saboda Sadiya Haruna tana wani abu mara kyau…ku ‘yan Hisban idan na ce zan kira suna ba za a ji dadi ba."
A cewar ministan, dalilin da ya sa gwamnati ta dauki tsawon lokacin kafin ta tabbatar da mutuwar Shekau shi ne, tana so ta samu tabbacin cewa lallai ya mutu kafin ta bayyana matsayarta.
Tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce dalilin da ya sa ‘yan siyasa ke haifarwa da Najeriya matsaloi shi ne, yadda ake bari kowa da kowa yake shiga harkar siyasa.
Ibeawuchi Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da Umezirike Onucha, wadanda kusoshi ne a jam’iyyar ta PDP suka shigar da karar.
Dan shekara 28, Lukaku ya zura kwallonsa ne a minti na 15 da fara wasa, sannan Reece James ya biyo da kwallo ta biyu a minti na 35.
Breaker ya rera wakar ‘Jaruma’ kana sun cashe a wakar ‘Da Ma’ da Namenj ya yi wacce ya gayyato Breaker suka yi tare.
Jihar Kaduna ta kasance daya daga cikin jihohi da ke fama da matsalar masu garkuwa da mutane a arewacin Najeriya.
Kama mutumin na zuwa ne, a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar ‘yan fashin daji da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa, musamman a arewa maso yammacin kasar.
A farkon watan nan, Messi ya yi ban kwana da kungiyar Barcelona da ya kwashe tsawon shekara 21, inda ya yi ta zub da hawaye a wani taron manema labarai da aka shirya don yi ban-kwana da shi.
Domin Kari