Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya karbi rahoton kwamitin da aka kafa don binciken zargin da ake yi wa Abba Kyari kan karbar cin hanci a hannun Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi.
Shugaban kwamitin binciken DIG Joseph Egbunike ne ya mika rahoton ga Akali Baba a ranar Alhamis kamar yadda wata sanarwa da kakakin hedkwatar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya fitar.
“Rahoton ya kunshi duk bincike kan lamarin, hujjoji, da kuma bahasin da DCP Abba Kyari ya bayar da na sauran mutanen da lamarin ya shafa.” Sanarwar ta ce.
Shugaban ‘yan sandan Najeriya Alkali Baba, ya yabawa kwamitin da wannan aiki da ya yi, yana mai cewa dalilin kafa kwamitin shi ne, a gudanar da sahihin bincike wanda zai taimakawa rundunar ‘yan sanda daukan matakin da ya dace.
“Za a yi kyakkyawan nazari kan shawarwarin da rahoton ya kunsa sannan daga nan a mika shi ga inda ya dace don daukan mataki na gaba.”
Kyari babban jami’in dan sanda ne a Najeriya, mai mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda. Ya kuma jagoranci wani sashen tattara bayanan sirri kan masu aikata manyan laifuka.
Hushpuppi na fuskantar shari’a a Amurka kan ayyukan da suka shafi damfara ta yanar gizo inda yayin binciken sa da ake yi aka zargi Kyari da taka rawa a wata badakalar dala miliyan 1.1 da Hushpuppi ya yi.
Dalilin kenan da ya sa hukumar da ke hukunta manyan laifuka ta FBI a Amurka ta nemi a mika mata Kyari.
A ranar 2 ga watan Agusta rundunar ‘yan sandan ta kafa kwamitin binciken Kyari.