Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu tana kan bakarta dangane da hani da ta yi kan biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.
Ministan yada labor da al’adu Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka a lokacin ziyarar da ya kai Washington a Amurka.
“Matsayar gwamnati ita ce, kada kowa ya biya kudin fansa don ceto ‘ya’yansa, na san wannan abu mai wuya ne ga iyaye, amma a karshe idan aka biya, hakan zai rika mayar da hannun agogo baya.” In ji Mohammed.
Ministan ya kara da cewa, idan ana biyan masu garkuwa kudin fansa, hakan zai sa lamarin ya zama kamar sana’a ko kuma ya zama tamkar wata hanya ta tafiyar da wata kungiyar masu aikata manyan laifuka.
“Bisa irin bayanan da muka tattara, wadannan masu garkuwa da mutanen, kan yi amfani da kudaden fansa ne wajen sayen makamai.”
A cewarsa, a ‘yan makonnin da suka gabata, dakarun Najeriya sun yi ta lugudan wuta akan maboyar ‘yan bindigar yana mai cewa ana samun nasara a yakin da ake yi.
Sai dai Mohammed ya kara da cewa, duk da matakan da ake dauka na far wa ‘yan bindigar, akwai wasu hanyoyi da ake bi ta bayan fage don shawo kan matsalar tsaron, abin da ya ce ba bakon abu ba ne a irin wannan yanayi da aka tsinci kai a ciki.
Najeriya, musamman a arewaci, na fama da matsalar masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, lamarin da ya kan kai ga asarar rayuka da dumbin dukiyoyi.
Biyan Kudin Fansa Ga 'Yan bindiga Na Mayar Da Hannun Agogo Baya - Lai Mohammed
Dalilin Da Ya Sa Ba Za Mu Hukunta ‘Yan Boko Haram Da Ke Mika Wuya Ba
A ‘yan makonnin baya-bayan nan, daruruwan mayakan Boko Haram sun yi ta mika wuya a yankin arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya sa jama’a da dama suka sa ido su ga yadda hukumomi za su yi da su.
Ko a makon da ya gabata, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagan Umara Zulum, ya bayyana mawuyacin halin da suka shiga kan matakin da ya kamata su daukan kan dumbin mayakan da ke mika wuya.
Akwai dai ‘yan Najeriya da dama da ke da ra’ayin cewa ya kamata a hukunta mayakan da ke mika wuya, idan aka yi la’akkari da irin barnar da ake zargin sun tafka cikin shekara 12 da kungiyar take kai hare-hare.
Sai dai a hirar da aka yi da shi, Ministan yada labaran ya ce akwai dokoki da ka’aidoji da aka shimfida na kasa da kasa kan yadda ya kamata a tafiyar da duk wanda ya mika wuya a lokacin yaki.
“Akwai dokoki da ka’idoji da aka shimfida na kasa da kasa kan yadda ake tafiyar da fursunonin yaki, ba za ka harbe su nan take ba ko kashe su.”
Da aka tambayi Lai Mohammed dalilin da ya kira mayakan Boko Haram da suka mika wuya a matsayin fursunonin yaki sai ya ce:
“Bisa dokar kasa da kasa, fursunonin yaki ne, duk wanda ya mika wuya, dokar kasa da kasa ba ta yarda ka jera su ka harbe su ba.
“Abin da kawai ake so a yi shi ne kamar yadda ake yi a ko ina a duniya, idan sun mika wuya, su tabbatar sun mika makamansu sannan a binciki labarinsu.” In ji ministan yada labaran.
Sai dai ya musanta rahotanni da ke cewa, ana kokarin a dauki wadannan mayakan da suka mika wuya a rundunar sojojin kasar.
“Babu wani shiri na kokarin a dauke su a aikin soja, sam babu kamshin gaskiya a wannan labarin.”