Ita dai kungiyar ta IPOB ta sha musanta hannu a kisan jami’an tsaron Najeriya da hare-hare da ake kai wa a kudu maso gabashin kasar.
Sai dai masu sharhi a fagen kwallon kafa na ganin, ita ma West Ham ba kanwar lasa ba ce, suna masu cewa, komai na iya faruwa a wasan.
Dan wasan Young Boys Siebatcheu ne ya ceto kungiyarsa gab da ana shirin kammala wasan bayan karin lokaci da aka yi.
Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar sun sace basaraken ne da yammacin ranar Talata akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Rahotanni sun ce 'yan Najeriya shida da ake nema, sunayensu sun fito ne cikin jerin mutum 38 daga kasashe daban-daban da kasar ta ayyana cewa tana farautarsu ruwa a jallo.
“Ina sane da cewa akwai matsalolin da ke shafar ayyukan da muke yi a sassan kasar nan, amma ina muku albishir da cewa, ana kan daukan matakan da za su kawo karshen wadannan kalubale.”
Ole Gunnar Solskjaer ya kuma yi fatan idan Manchester United ta lashe kofuna, hakan zai ba Paul Pogba kwarin gwiwar ci gaba da zama a kulob din.
Tankar man ta fadi ne yayin da direbanta ke kokain shiga shataletalen da ake kira Maidoki a birnin Yola da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.
“Mutumin arziki wallahi, mai kirki, ban taba ganin fushinka ba. Ba ka taba fada da kowa ba. Ga ban dariya. Allah ya maka rahama.” In ji Mansura Isah.
Karin hasken da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi na zuwa ne kasa da sa'a 24 bayan da ta wallafa bidiyon farko wanda ya janyo muhawara.
A shekarar 2020, an taba yanke wa Forest kafa bayan tsawon lokaci da ya kwashe yana fama da wata jinya.
A makon da ya gabata aka katse hanyoyin sadarwa a Zamfara a wani mataki na shawo kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar.
Ofishin jakadancin Saudiyya a Washington ya jima yana nuna goyon bayan a fitar da bayanan sirrin don a kawo karshen zargin da ake yi wa masarautar, wanda ya ce “ba su da tushe.”
Manchester United ta lallasa Newscastle da ci 4-1 a wasan wanda aka buga a Old Trafford.
Kusan mutum 3,000 ne suka mutu a ranar ciki har da ma’aikatan kashe gobara da ‘yan sanda da suka kai dauki.
Mun yi waiwaye kan yadda aka kai wadannan hare-hare da suka sa Amurka ta mamaye Iraqi da Afghanistan domin yakar ayyukan ta’addanci.
An jima ana neman Modu ruwa a jallo, saboda irin rawar da yake takawa wajen kitsa ayyukan ta’addanci a cewar sojojin Najeriya.
Brazil ce a saman teburin da maki 24, Argentina a matsayi na biyu da maki 18 sai Uruguay da maki 15 baya ga Ecuador mai maki 13 da Columbia mai maki 13 ita ma.
Domin Kari