Rahotanni daga Najeriya na cewa, shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya Abdulrasheed Bawa ya yanke jiki ya fadi.
Lamarin ya faru ne a fadar shugaban kasa, yayin da Bawa yake jawabi a wani taro da ke gudana a Abuja.
Bayanai sun yi nuni da cewa, Bawa na cikin magana sai aka ji ya shiru, jim kadan bayan hakan sai aka ka ga ya kare fuskarsa da hannunsa yana mai cewa a yi hakuri ba zai iya ci gaba da magana ba.
Nan da nan ministan sadarwa Dr. Isa Ali Pantami da was manyan jami'an gwamnati, da ke halartar taron, suka tashi suka rike shi don su zaunar da shi, a yayin hakan ya yanke jiki ya fadi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Rahotanni sun ce bayan an fitar da shi daga dakin taron, mai jagorantar taron wanda aka shirya kan karbar katin dan kasa ya bayyana cewa babu wata fargaba Bawa na cikin koshin lafiya.
Gidan talabijin na Channels ya ce minista Pantami ne ya dawo dakin taron ya ce shugaban na EFCC yana cikin koshin lafiya.
A watan Fabrairun 2021 Shugaba Buhari ya nada Bawa dan shekara 40 a matsayin sabon shugaban hukumar ta EFCC.
Mohammed Umar, wanda darekta ne a hukumar ya maye gurbin Ibrahim Magu a matsayi na wucin gadi, bayan da aka kama Magu a watan Yuli bisa zargin cin hanci da rashawa da ya musanta.