Mai masaukin baki wato Liverpool ta fara wasan ne da zafi-zafi inda har ta zura kwallon farko bayan da Alexander-Arnold ya sa Fikayo Tomori na Milan ya ci gida,
Mohamed Salah ya samu wata dama ta bugun fenariti, sai dai mai tsaron ragar Milan Mike Maignan ya kabe ta.
Bayan wani kukan kura da ta yi, duk da cewa Liverpool ta rutsa ta, Milan ta zura kwallaye biyu kusan a jere.
Ante Rebic ne ya fara farke kwallon farko a minti na 42, sannan jim kadan bayan hakan Brahim Diaz ya kara wata a minti na 44.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Milan ta saka wata kwallo da alkalin wasa ya ki amincewa da ita gabanin Salah ya dauki fansar fenaritin da ya zubar a minti na 49 – lamarin da ya kai wasan 2-2.
Sai dai kyaftin din Liverpool Jordan Henderson, ya kwato Liverpool da wata kwallo da ya zura a minti na 69, abin da ya kai wasan ga 3-2 ya kuma ba mai masaukin baki a Anfield nasara a karshe.