Tawagar ‘yan wasan Young Boys ta kasar Switzerland ta shammaci Manchester United ta kasar Ingila da ci 2-1 a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta UEFA.
Dan wasan Young Boys Siebatcheu ne ya ceto kungiyarsa gab da ana shirin kammala wasan bayan karin lokaci da aka yi.
Gabanin kwallon ta Siebatcheu, wasan yana ci 1-1.
Cristiano Ronaldo ne ya fara ci wa United kwallo a minti na 13 a wannan wasa nata da ya kasance na farko a sabuwar kakar wasa ta Champions League.
Sai dai ana shirin tafiya hutun rabin lokaci alkalin wasa ya ba Wan- Bissaka jan kati bayan da ya same shi da laifin yin shigar mugunta ga dan wasan Young Boys Martins.
Hakan ya sa Manchester United ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10, abin da Young Boys ta yi amfani da shi ta farke kwallon.
Dan wasan Young Boys Ngamaleu ne ya farke kwallon farko a minti na 66.
Ole Gunner Solskjaer ya cire Ronaldo a wasan, ya maye gurbinsa da Jesse Lingard, wani abu da masu fashin baki suka ce dabara ce ta kare lafiyar fitaccen dan wasan.
Ko da yake, wasu na ganin sauyin ya taimaka wajen kayen da United ta sha a hannun Young Boys.
Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?