Shugaba Joe Biden, ya yi gargadin cewa, akwai yiwuwar Rasha ta kai hari kan rumbun adana bayanai a wasu wurare a Amurka ko kuma ta yi amfani da makamai masu guba a Ukraine yayin da mamayar da Rashar ta yi wa kasar ta Ukraine ta doshi wata guda.
A dai ranar Talata, 29 ga watan Maris kasashen biyu, wadanda makwabtan juna ne a yankin yammacin Afirka, za su sake haduwa a Abuja, babban birnin Najeriya.
“Dole sai mun hada kanmu wuri guda, muna Allah wadai tare da yakar irin wannan al’amari, shi ne kadai za mu iya kawo karshen wadannan rikice-rikice.”
Taron zai ba jam’iyyar damar zaben shugabannin da za su tafiyar da ragamar jam’iyyar a matakai daban-daban na kasa da kuma tsara yadda za su tunkari zaben 2023 da ke tafe.
Annobar COVID-19, ta sa jama'a da dama sun kauracewa wuraren aiki a Amurka, lamarin da ya sa wasu masana'antu suka fara maye gurbin mutanen da mutum-mutumi don gudanar da ayyunsu.
Shirin Duniyar Amurka na wannan mako ya tabo batun tallafin biliyoyin daloli da Amurka za ta bai wa Ukraine, bayan da Majalisar Dokoki ta amince da shirin tallafin, yayin da Rasha ke ci gaba da kai mamaya sannan Ukraine ba tare da ta takale ta ba.
Kididdiga ta nuna cewa cikin minti 16 Benzema ya zura duka kwallayen ukun a ragar Paris Saint Germain.
A watan Oktoban 2020 gwamna Umahi da mataimakinsa Igwe suka koma jam’iyyar APC mai mulkin kasa.
Bisa alkaluma da ma’aikatar kidayar jama'a ta Amurka ta fitar, akwai akalla ‘yan kasar Ukraine dubu 105 da ke zaune a Amurka, wadanda ba 'yan kasa ba, 2,000 daga cikinsu, dalibai ne da ka iya cin gajiyar shirin na samar a kariya na TPS.
Garin na Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine, na da tazarar kilomita 30 tsakaninsa da Rasha.
“Tawagar farko za ta iso Najeriya a ranar Alhamis 3 ga watan Maris.” In ji ma'aikatar harkokin wajen Najeriya.
Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum dubu 520 ne suka fice daga Ukraine, wadanda mafi akasarinsu suka doshi Poland.
“Yana da muhimmanci a rika tafiyar da kowa da kowa a matsayin daya, ta hanyar mutuntawa da girmamawa.” In ji Garba Shehu.
Shugaban Amurka Joe Biden, a ranar Alhamis ya bayyana karin takunkumi akan Rasha, bayan da ta kai mamaya a kasar Ukraine da sanyin safiyar ranar ta Alhamis. Yau batun da shirin Duniyar Amurka na wannan mako ya yi nazari akai kenan tare da Mahmud Lalo
Buhari na ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Nasarawa, inda ya je don kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule ta yi.
“Ina so na yi kira ga gwamnatin Najeriya, da ta yi iya bakin kokarinta wajen kwaso ‘yan kasarta, wadanda akasarinsu dalibai ne.” Atiku ya ce.
Baya ga wasan na Atletico da United, Benfica za ta karbi bakuncin Ajax a wasa na biyu da za a buga a wannan Laraba.
Matsalar kashe-kashen da ake yi don yin tsafi ta yi kamari a ‘yan kwanakin nan a Najeriya musamman a kudancin kasar.
Matsalar yawan kashe-kashen da ake yi don yin tsafi ta yi kamari a ‘yan kwanakin nan a Najeriya musamman a kudancin kasar.
Wani babban wasa da masu sha’awar kwallon kafa suka kasa suka tsare shi ne wasan Atletico Madrid da Manchester United inda ‘yan wasan kasar Uruguay Luis Suarez da Edison Cavani za su hadu.
Domin Kari