Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebonyi: PDP Na Shirin Mika Sunayen Gwamna Da Mataimaki Bayan Da Kotu Ta Sallami Umahi


Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi (Gwamnatin jihar Ebonyi)
Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi (Gwamnatin jihar Ebonyi)

A watan Oktoban 2020 gwamna Umahi da mataimakinsa Igwe suka koma jam’iyyar APC mai mulkin kasa.

Hedkwatar jam’iyyar PDP a Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba, za ta bayyana sunayen wadanda za su tsaya mata a mukamin Gwamna da mataimaki a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin kasar.

A ranar Talata wata kotun tarayya a Abuja ta yanke hukuncin cire Gwamna Dave Umahi da mataimakinsa Eric Igwe, saboda sheka da suka sauya zuwa jam’iyyar APC.

Yayin da yake yanke hukuncin, Alkali Iyang Ekwo ya ce jam’iyyar ce ta ci zabe ba dan takara ba, saboda haka, ba su da hurumin su ci gaba da zama a mukamansu tun da sun sauya sheka.

Alkali Ekwo ya kara da cewa, babu yadda za a yi nasarar da suka samu a zaben ta bi su zuwa jam’iyyar da suka koma, saboda jam’iyya ce ke cin zabe ba dan takara ba.

Umahi da Igwe ne suka lashe zaben gwamnan jihar ta Ebonyi da aka yi a watan Maris din 2019 karkashin inuwar jam’iayyar PDP.

Shugaba Buhari (hagu) da gwamnan Ebonyi David Umahi yayin wata ziyara da kai wa Abuja (Facebook/David Umahi)
Shugaba Buhari (hagu) da gwamnan Ebonyi David Umahi yayin wata ziyara da kai wa Abuja (Facebook/David Umahi)

Amma sun sauya sheka a watan Oktoban 2020 inda suka koma jam’iyyar APC mai mulkin kasa.

Ba a kuma jima ba sai kakakin majalisar dokokin jihar da wasu mambobin majalisar jihar 15 su ma suka sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Alkalin wanda ya yi amfani da sashe na 221 na kundin tsarin mulkin Najeriya, ya umarci PDP da ta yi maza ta aikawa hukumar zabe ta INEC sunayen wadanda za ta maye gurbin mukamin Gwamna da na mataimakinsa saboda a gurdanar da sabon zabe.

Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP a Najeriya (Facebook/Daily Post)
Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP a Najeriya (Facebook/Daily Post)

Kazalika kotun ta umarci Umahi da mataimakinsa da su biya dukkan kudaden albashin da aka biya su tun daga lokacin da suka sauya sheka zuwa yanzu.

“Ba za mu yi hanzarin fitar da sunayen ba, amma nan ba da jimawa ba za mu fitar da sunayen ga manema labarai.” In ji shugaban PDP a Najeriya Iyorchia Ayu.

Sai dai yayin wani taron manema labara a Abakaliki, Umahi ya ce har yanzu shi ne gwamnan jihar ta Ebonyi, inda ya zargi PDP da hannu a hukuncin da kotun ta yanke.

XS
SM
MD
LG