Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a jihar Kaduna da ke arewacin kasar wadanda suka yi sanadiyyar mutane da dama.
A karshen makon da ya gabata, ‘yan bindiga suka far yankin masarautar Kagoro suka kashe adadin mutanen da gwamnatin jihar Kaduna ta ce ya kai 34.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya ce, kashe-kashen da ake yi a kasar, abu ne da ba za a lamunta ba.
“Wannan hari da aka kai na baya-bayan nan a Kaduna inda mutane da dama suka mutu, abu ne da ba za mu lamunta ba, muna kuma Allah wadai da shi.”
“Bai kamata a ce mun kai wani shalli da ran da adam ya zama ba a bakin komai yake ba.” Atiku ya ce cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa a ranar Larabar da ta gabata, ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu “a wannan mummunan hari.”
“Dole sai mun hada kanmu wuri guda, muna Allah wadai tare da yakar irin wannan al’amari, shi ne kadai za mu iya kawo karshen wadannan rikice-rikice.”
Da yake lissafo manufofinsa a dandalin taron bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa, Atiku ya ambato batun tsaro a matsayin daya daga cikin abubuwa biyar da zai tunkara idan ya samu nasara a zaben na 2023.
A zaben 2019, Shugaba Muhammadu Buhari da yake shirin kammala wa’adinsa na biyu, ya ka da Atiku a takarar da ya yi karkashin jam’iyyar PDP mai adawa.