Babbar jami’yyar adawa ta PDP a Najeriya, ta yi kira ga hukumar zaben kasar ta INEC da ta guji tura jami’anta don sa ido a babban taron jam’iyyar APC mai mulki da za a gudanar a karshen makon nan tana mai cewa yin hakan zai sabawa dokar kasa.
A ranar Asabar APC za ta gudanar da babban taronta na kasa a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Taron zai ba jam’iyyar damar zaben shugabannin da za su tafiyar da ragamar jam’iyyar a matakai daban-daban na kasa da kuma tsara yadda za su tunkari zaben 2023 da ke tafe.
Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis dauke da sa hannun Sakataren yada labaranta, Hon. Debo Ologunaba, PDP ta yi wa hukumar zabe ta INEC garagdin cewa da kada ta halarci taron ko ta tura masu sa ido.
A cewar PDP, yin hakan, zai sabawa dokar kasa.
“Zuwan INEC wannan babban taron jam’iyyar, ya zama ta tsallake ayyukan da kundin tsarin mulki na 1999 ya tanada mata tare take dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima ta 2022.” Sanarwar ta ce.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Talatar da ta gabata dauke da sa hannun kakakin shugaban kasa Femi Adesina, gwamnatin Buhari ta zargi jam’iyyar ta PDP da kokarin neman hanyoyin da za su ta da husuma a kasar.