An yi ta ce-ce-ku-ce kan halin da Tinubu yake ciki bayan da ya gaza halartar taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a tsakanin jam’iyyun siyasar kasar a makon da ya gabata a Abuja.
Cibiyar da ke sa ido kan aukuwar bala’in guguwa a Amurka, ta yi hasashen guguwar ta Iyan, za ta sauka a jihar ta South Carolina a yau Juma’a dauke da karfin da ya kai mataki na daya.
“Yanzu haka muna shirin gudanar da zabe a watan Fabrairu mai zuwa, taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi (badi) a karo na 78, bakuwar fuska za ku gani a nan yana magana da yawun Najeriya.” In ji Buhari.
A ranar Litinin din da ta gabata, Ma’aikatar Tsaron Isra’ila ta fitar da wata sanarwa inda ta ce “mai yiwuwa," sojojinta ne suka harbe Abu Akleh bisa kuskure, a lokacin da suke musayar wuta da wasu Falasdinawa masu dauke da bindiga.
Malam Mamu ne ya shiga tsakani wajen karbo kusan mutum 20 daga cikin fasinjojin jirgin kasa da ‘yan bindiga suka sace a watan Maris din wannan shekara.
A ranar Talata ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol suka kama Mamu a birnin Alkahira da ke Masar, a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa aikin Umrah a kasar Saudiyya tare da ahlinsa.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilin rusa majalisar zartarwar ba, amma ta ce nan ba da jimawa ba za a sake kafa wata majalisar.
Wannan yajin aiki ka iya haifar da matsalar karancin man a yankin arewacin kasar ciki har da Abuja, babban birnin Najeriya kamar yadda masu lura da al'amura suka bayyana.
A wani taron kasa da aka kaddamar da shirin yaki da masu aikata manyan laifuka wanda ya gudana a jihar Pennsylvania, Biden ya takawa ‘yan Republican burki kan kalaman da suke yi, wadanda ya ce ba su dace ba.
Ita dai jam'iyyar APC mai mulki ta ce lokaci kawai take jira ta lashe zaben wanda za a yi a watan Fabrairun badi.
“Ba za kuma mu manta da yadda Gorbachev ya yi ta yekuwar tarayyar Soviet da Amurka su rusa makaman nukiliyansu ba, a lokacin wani zama da suka yi da tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan.”
Akalla ‘yan sanda hudu aka kashe a farkon watan Agusta a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, a wani hari da ake zargin ‘yan aware ne suka kai.
“Da ma mu akidarmu, duk inda za a yi zalunci, babu adalci, babu mu a wurin. Da a ce kawai wata bukatata ce ko bukatar wasu daga cikin wadanda muke shugabanci tare da su, ai da wannan gayyar ta al’umar Kano, da ba su mana biyayya ba.” In ji Shekarau
Kaddamar da ofishin jami'yyar na zuwa ne, kwanaki uku bayan da rahotanni suka nuna cewa ‘yan sanda a jihar sun rufe ofishin na NNPP da ke garin Maiduguri.
Wannan lamari ya sa ana tunanin Trump ya karya doka kuma zai iya fuskantar tuhuma a kotu yayin da lauyoyinsa suka nemi wata kotu ta dakatar da nazarin da ake yi kan takardun.
Cikin wani sako da ya wallafa a watan Yuni a shafinsa na Twitter, Atiku ya tabbatar da cewa jam’iyyar tana kokarin dinke barakar da ta kunno kai a jam'iyyar, yana mai cewa, za a sasanta komai.
A watan Yulin da ya gabata, Osinbajo ya sanar da cewa an yi masa tiyata a kafa sanadiyyar wani ciwo da ya ce ya jima yana fama da shi.
“NFF ba ta da hannu a wannan akasi da aka samu, domin ta shirya tsaf don tarbar tawagar ‘yan wasan a Abuja, gabanin a samu tangarda a tafiyar ta su.” In ji Sanusi.
Mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce, likitocinsa za su yi karin bayani a nan gaba.
Domin Kari