Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda ‘Yan Wasan Falconets Na Najeriya Suka Makale A Turkiyya


'Yan wasan Falconets na Najeriya (Facebook: NFF)
'Yan wasan Falconets na Najeriya (Facebook: NFF)

“NFF ba ta da hannu a wannan akasi da aka samu, domin ta shirya tsaf don tarbar tawagar ‘yan wasan a Abuja, gabanin a samu tangarda a tafiyar ta su.” In ji Sanusi.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta yi karin haske kan jinkirin da aka samu wajen komawar ‘yan wasan Falconets gida inda suka makale a Istanbul, babban birnin Turkiyya, bayan da aka cire su a gasar cin kofin duniya ta mata ta ‘yan kasa da shekaru 20.

‘Yan wasan Netherland sun doke Falconets da ci 2-0 a Costa Rica, kayen da ya fitar da su a gasar.

Rahotanni sun yi nuni da cewa ‘yan wasan za su bi ta kasar Colombia zuwa Istanbul daga nan sai su hau jirgi zuwa Abuja.

Sai dai hakan bai yi wu ba, saboda kamfanin jirgi na Turkey Airline ya jinkirta tashin jirginsu daga Colombia zuwa Istanbul, lamarin da ya sa suka gaza riskar jirgin da zai kai su Abuja daga babban birnin na Turkiyya.

Hakan kuma ya kai ga makalewarsu a birnin har tsawon sa'a 24.

An dai yi ta yada wasu hotuna a kafafen sada zumunta da suka nuna ‘yan wasan kwance a kasa a filin tashin jiragen na Istanbul, abin da ya kai ga ‘yan Najeriya suka yi ta suka akai.

Sai dai hukumar kwallon kafa ta NFF ta ce ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an ba ‘yan wasan takardar visa mai gajeran zango don su je su kama otel su kwana kafin jirginsu ya taso amma abin ya ci tura.

“Hakan bai yi wu ba saboda, an fada mana cewa, Turkiyya ta cire Najeriya a cikin jerin kasashen da ake ba ‘yan kasarta visa mai gajeran zango nan take idan suka sauka a Turkiyya.

“Hakan ya sa kamfanin na Turkiyya ya dauki ‘yan wasan ya ajiye su a wani wurin kwanciya a filin tashin jiragen, suka ba su tikitin karbar abinci.” In ji Sakatare Janar na hukumar NFF, Dr. Mohammed Sanusi cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin hukumar na Facebook a ranar Laraba.

Hukumar ta NFF ta kara da cewa, hukumar FIFA, wacce ita take da alhakin sayawa ‘yan wasa tikiti, ita ma ba ta hangi za a samu irin wannan tangarda ba.

“NFF ba ta da hannu a wannan akasi da aka samu, domin ta shirya tsaf don tarbar tawagar ‘yan wasan a Abuja, gabanin a samu tangarda a tafiyar ta su.” In ji Sanusi.

'Yan wasan na Falconets sun lashe dukkan wasanninsu na farko a rukunin C inda suka kare da maki 9 inda daga baya Netherland ta fitar da su a gasar.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG