Shirin har ila yau, ya yi duba kan wani sabon rahoto da aka fitar, wanda ya kara tabbatar da cewa 'yan sandan garin Uvalde a jihar Texas, sun yi sakaci wajen kai dauki yayin da wani dan bindiga ya shiga wata makarantar firamare ya harbe yara 19 da malamai biyu a watan Mayu.