Babban Sufetan ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ce ba za su lamunci hare-haren da ake yawan kai wa akan jami’ansu ba, yana mai cewa yin hakan babban laifi ne da ya sabawa doka.
Cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta fitar a ranar Litinin dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a, CSP Olumuyiwa Adejobi, Alkali Baba ya nuna takaicinsa kan yadda ake yawan kai harin kan jami’an tsaro da ke sanye da kayan sarki a sassan kasar.
“Sufeta Janar ya yi gargadin cewa, daga yanzu, rundunar ‘yan sandan ba za ta amince da duk wani hari da aka kai akan jami’anta ba, saboda muna daukar rayukansu da matukar muhimmanci.
“A dalilin haka, babban Sufeta Janar, ya bai wa dukkan rundunonin kasar umarnin cewa, daga yanzu, duk wanda aka kama da laifin kai hari kan wani jami’in tsaro, a tabbata a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.” Sanarwar ta ce.
A baya-bayan nan, ana yawan samun rahotannin da ke nuni da cewa ana kai hari kan jami’an tsaro musamman ‘yan sanda a sassan kasar.
Akalla ‘yan sanda hudu aka kashe a farkon watan Agusta a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya a wani hari da ake zargin ‘yan aware ne suka kai.
A lokuta da dama, ‘yan awaren kungiyar ta IPOB, kan nesanta kansu da ire-iren wadannan hare-hare.