Sai dai akwai alamu da ke nuni da cewa, babu makawa Biden shi zai sake lashe tikitin tsayawa jam’iyyar ta Democrat takara a zaben na badi.
Sannan za ku ji cewa rundunar sojin saman Amurka ta kaddamaR da bincike kan yadda wani sojanta ya kai ga samun wasu takardun bayanan sirrin kasar da ya kwarmata a shafukan sada zumunta.
Trump ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa da kuma mu'amullar da Stormy Daniels ta yi zargin sun yi a shekarar 2006.
Amurka ta kuma jajantawa al'umar Turkiyya da Syria da suka fuskanci ibtila'in girgizar kasa da kuma Musulmin China da na Myanmar da ake muzgunawa.
A karshen makon da ya gabata, hukumomin da ke kula da hadahadar kudade a Amurka, suka karbe ragamar tafiyar da bankunan Silicon Valley da Signature da suka durkushe.
Kotun har ila yau ta ba da izinin kama kwamishiniyar kare hakkin yara a ofishin shugaban kasar ta Rasha, Maria Alekseyevna Lvova Belova, wacce ita ma ake zargin ta da hannu a lamarin.
Har yanzu wasu 'yan Najeriya na dari-dari wajen karbar tsofaffin takardun kudin Najeriya (Naira) sama da kwanaki goma bayan umurnin babban bankin kasar CBN na tabbatar da hallarcin kudaden bisa umarnin kotun koli.
Sai dai duk da umurnin da babban bankin ya bayar, rahotanni sun ce har yanzu akwai wasu ‘yan Najeriyar da ke dari-darin karbar kudaden.
Yayin da wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ke shirin karewa , jama’a da dama za su zura wa magajinsa ido don ganin yadda zai shawo kan matsalar ta hare-hare a Najeriya.
Sai dai Amurkar ta ce akwai bukatar hukumar zabe ta INEC ta yi gyara a fannonin da aka samu kura-kurai a zaben shugaban kasa kafin zaben gwamnoni da za a yi ranar 11 ga watan Maris.
Hukumar zabe ta INEC ta ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba zai iya gabatar da korafinsa a gaban kotu.
A ranar Litinin wasu daga cikin wakilan jam'iyyun na bangaren 'yan adawa suka fice daga zauren tattara sakamakon zaben bayan da suka nuna rashin gamsuwar kan abin da ke faruwa.
Har yanzu hukumomin jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ba su fayyace musabbabin gobarar ba, wacce ta lakume shaguna da dama.
Mambobin tawagar sun kwashe kwanaki 11 suna taimakawa da na'urorin gano inda mutane suka makale a girgizar kasar wacce ta kashe sama da mutum dubu hudu.
Yayin da a Najeriya aka tunkari babban zaben 2023, wasu ‘yan gudun hijra da ‘yan bindiga suka raba da muhallansu a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin kasar, sun koka da rashin samun katin zaben da za su kada kuri’unsu.
A ranar Juma’a majalisar ta yi wani taron gaggawa don tattauna halin da kasa ke ciki a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar ta PDP a Kano a baya-bayan nan, lamarin da ya sa ta rabu gida biyu tsakanin Wali da Abacha.
A ranar 15 ga watan Fabrairu kotun kolin za ta yi zama na gaba don ci gaba da sauraren karar.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, wanda shi zai jagoranci kwamitin ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja.
Hukumar NUC da ke kula da jami’o’in Najeriya ta ba shugabannin jami’o’in kasar umurnin su rufe sai bayan zabe.
Domin Kari