Zubar dusar kankara da ruwan sama da kuma mummunar guguwa da ake fuskanta a sassan Amurka, na daga cikin dalilan da suka sa jama'a suka kauracewa cibiyoyin ba da gudunmawar jini a Amurka a cewar Red Cross.
Sannan shirin ya duba muhawara ta biyar da 'yan takarar da ke neman tikitin jam'iyyar Republican suka yi a karo na biyar - wato tsakanin - Nikki Haley da Gwamna Ron DeSantis na jihar Florida
Aikin layin dogon ko na jirgin kasa zai tashi daga Angola mai arzikin mai inda zai ratsa tsakiyar nahiyar Afirka.
Jihohin yankin na arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihar Borno, sun kwashe sama da shekara goma suna fama da matsalar mayakan Boko Haram.
Dukkanin 'yan majalisar da kotun ta soke zaben nasu 'yan jam'iyyar PDP ne, abin da ke nufin jam'iyyar ta rasa rinjayen da take da shi a mjalisar dokokin.
Daya daga cikinsu ta ce Diddy ya taba zuba mata kwayoyi a abinci ya kuma yi mata fyade har da dauka a bidiyo ba tare da saninta ba
Ana tuhumar Brazil da laifin gazawa da samar da cikakken tsaro a wasan da ta tsara.
Kungiyar mai suna EAC a takaice, na dauke da kasashen Burundi, Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Kenya, Rwanda, Sudan ta Kudu, Tanzania da kuma Uganda.
Abin tambaya a nan shi ne, wacce irin rawa wannan muhawara ta zubar da ciki wacce ke zama zazzafa za ta taka a zaben shugaban kasa da za a yi badi?
Shugaban tsare-tsare a kungiyar tarayyar turai ta EU Josep Borrel, shi ma ya fada a ranar Litinin cewa, shugabanin kungiyar ta EU za su goyi bayan duk wani kira da zai ba da damar “a dakatar da fadan saboda al’amari na jin-kai” domin a samu shiga da kayayyakin agaji a yankin na Gaza.
Sannan daga cikin manufofin ziyarar da Biden din ya kai Isra’ila a ranar Laraba, har da tunkarar batun samar da maslaha kan yadda za a bude hanyar gudanar da ayyukan jin-kai a yankin zirin Gaza.
Shin me McCarthy ya yi aka tsige shi, wane tasiri hakan zai yi kan siyasar Amurka musamman kan zaben shugaban kasa da ke tafe a shekara mai zuwa? Ku saurari shirin domin jin karin bayani.
Ko da yake, ba a fayyace abin zai yi magana a kai ba, amma wasu na ganin taron manema labaran bai rasa nasaba da batun takardun karatun Bola Ahmed Tinubu da Jami'ar Chicago da ke Amurka ta fitar.
Sannan za ku ji cewa, tsohon shugban Amurk Donald Trump, na shirin daukaka kara, bayan da wata kotun New York ta same shi da laifin zuzuta darajar kadarorinsa – wato ya kara musu kudi cikin shekaru da dama da ya kwashe yana harkokin kasuwancinsa – don amfanin kansa.
Domin Kari