A daidai lokacin da al'umomi a wasu sassan Jihar Kaduna ke fama da hare-haren 'yan-bindiga da sace-sacen mutane don neman kudin fansa, wasu al'umma a yankin karamar hukumar Birnin Gwari sun ce akwai wasu mutane da ake kira 'yan-Ansaru dake yawan zuwa garuruwan su dauke da manyan makamai.
Har yanzu dai 'yan'uwan wadanda 'yan-bindigan suka tare a hanya na ci gaba da binchiken inda 'yan'uwansu su ke yayin da wadanda suka tsira ke jinya a asibitoci daban-daban.
Babban bankin Najeriya ya ce dalar masarar da aka kaddamar a Jihar Kaduna alama ce cewa gwamnatin tarayya ta inganta noma ta yadda za a iya fitar da masara zuwa kasashen waje.
Kwana biyu da kai harin da 'yan-bindiga su ka yi a wasu garuruwan karamar hukumar Kaura da ke kudancin Kaduna, gwamnatin jihar ta fitar da sunayen mutanen da aka kashe da kuma asarar dukiyar da aka yi.
Kungiyar Kiristan Najeriya, CAN, ta ce 'yan bindiga sun kashe mutane sama da ashirin sannan su ka kone gidaje da dama a wasu unguwanni uku a masarautar Kagoro da ke kudancin Kaduna.
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce kalaman Jagoran 'yan bindiga Bello Turji na neman sulhu alamu ne cewa addu'o'in al'umma na karbuwa wajen kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a fadin jihar baki daya.
Biyo bayan kara tsawon yajin aikin Malaman Jami'o'in Najeriya har na watanni biyu ya sa kungiyar iyaye da Malaman makarantu ta kasa nuni da irin hadarin da Najeriya ka iya shiga idan ba a dauki mataki ba.
Kungiyar Malaman jami'a, shiyyar Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta dage kan cewa sai jami'ar ta kwace takardar shaidar digiri ta gwamnan jahar Kaduna saboda karbe ma ta filaye da kuma rufe katangarta da ya yi.
Shirin Manuniya na wannan mako ya yi dubi ne akan rikichin cikin gidan Jam'iyyar APC da kuma takaddamar shugabanchin kwamitin riko na Jam'iyyar APC a Kasa sai kuma maganar watsi da bukatar kwaskwarimar dokokin zabe da majalissar dattijai da sauran batutuwan siyasa.
Wata kungiya mai fafutukar samar da gwamnatoci na gari da kuma adalci wato Network For Good Governance and Justice ta ce idan har ana so a magance matsalolin Najeriya dole a hada kai da 'yan-jarida.
Gwamnatin jahar Kaduna ta ce an auna arziki ne da bama-baman da aka gano an dasa a yankin Kabala-West da Unguwan Romi ba su tashi cikin jama'a ba, amma da an yi asarar rayuka da dukiyoyi.
Kimanin watanni biyu da bada umarnin addu'o'i na musamman da kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta yi, Kungiyar ta ce ana samun nasarori game da matsalolin tsaro a Najeriya sai dai kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta ce gwamnati na bukatar kara damara idan tana son magance matsalar tsaro.
Tuni dai wannan murya ta kai kunnen mahukunta kuma har ma wasu daga cikinsu sun ziyarci tashar ta Kawo don bibiyar lamarin.
Ganin yadda hare-haren 'yan-bindiga ya yawaita a makarantu a shekarar bara, ya sa wata kungiya mai zaman kan ta shirya taron bita ga Malamai da dalibai don kare kawunan su daka hare-haren.
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce an kashe mutane 1,129) a fadin jihar Kaduna a bara, sannan an kiyasta cewa kullum akan sace mutane tara a fadin jihar.
Wasu al'umomin garuruwa 11 dake karamar hukumar Birnin Gwari, a jihar Kaduna, sun ce sun hada sama da naira miliyan 30 a matsayin kudin neman sasantawa da 'yan bindiga.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ayyukan cigaban da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa'i ya yi sun sa ya kasa kai kanshi gida duk da shekarun da ya yi a matsayin mazaunin Kaduna kafin zama shugaban Kasa.
Domin Kari