Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CAN Ta Ce 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Sama Da 20 Sun Kuma Kona Gidaje Da Dama


Rev John Joseph Hayab
Rev John Joseph Hayab

Kungiyar Kiristan Najeriya, CAN, ta ce 'yan bindiga sun kashe mutane sama da ashirin sannan su ka kone gidaje da dama a wasu unguwanni uku a masarautar Kagoro da ke kudancin Kaduna.

Yankin Kudanchin Kaduna dai na cikin yankunan da ke fama da hare-haren 'yan bindiga a jahar Kaduna duk kuwa da cewa 'yan kwanakin nan an sami sauki, sai dai kungiyar Kirista ta CAN, reshen jahar Kaduna, ta bakin shugabanata Rabaren John Joseph Hayab, ta ce sabon harin da aka kai yankin jiya Lahadi ya yi muni matuka.

Yanzu haka dai gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da saka dokar hana zirga-zirga a Kananan hukumomin Jama'a da Kaura biyo bayan wadannan hare-haren. Sai dai duk kokarin jin ta bakin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan din da ya bada wannan sanarwa ya ci tura, saboda bai amsa sakon da na tura mai ba har zuwa lokacin da wannan rahoto ke haduwa, ko da ya ke kuma ya sha bayyana kokarin da gwamnati ke yi game da wannan batu.

Sai dai kuma shugaban kungiyar Kirista na jahar Kaduna, Rabaren John Joseph Hayab ya ce ba su gamsu da kokarin na gwamnatin ba.

A lokuta da dama dai gwamna Nasiru Ahmed El-rufa'i na jahar Kaduna ya sha zuwa fadar shugaban Kasa don neman daukin tsaro, sai dai har yanzu matsalar tsaron ba ta kare ba.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
XS
SM
MD
LG