Jihar Zamfara dai na cikin jihohin Najeriya da su ke fama da hare-haren 'yan bindiga da sace mutane, sai dai ganin hirar da aka yi da Jagoran 'yan bindiga Bello Turji, ya sa kwamishinan tsaro na jihar, DIG Maman Ibrahim Tsafe mai ritaya, shedawa manema labaru cewa daman kofar sulhu na bude, sai dai kuma ba irin sulhun da aka yi ne a baya ba.
“A gaskiya ban ji maganar da Turji ya yi ba, amma dai kwamishinan labaru ya tabbatar ya yi magana, kila shima Turjin ya tuba, saboda shiriya ta Allah bata karewa, in Allah Ya tashi shiryaka ba shawara Yake yi da kowa ba, in dai har da gaske yake toh Allah shirya shi,” in ji Ibrahim Tsafe.
Shi kuwa kwamishinan Yada labaru na Zamfara, Hon. Ibrahim Magaji Dosara, wanda ya jagoranci taron manema labarun da jami'an gwamnatin jihar Zamfaran su ka kira a Kaduna, bayanin kalubalen tsaron da su ka gano ya yiwa manema labaru.
Ya ce akwai masu dafawa ‘yan bindiga baya wurin gudanar da wadannan ayyukan akwai kuma masu basu bayanan jama’a na sirri haka zalika akwai wadanda suke kaiwa ‘yan bindigan ababen bukatun su kamar bindigogi, albarusai, makamai, kayan abinci da sauran su suna kai musu a cikin daji.
Dosara ya kara da cewa akwai kuma wasu ‘yan siyasa dake amfani da bara-gurbin ‘yan jaridar waya suna yayata labarun karya domin su tada hankalin al’umma ko kuma a nunawa duniya Zamfara bata zaune lafiya, ya kuma ce gwamnan Zamfara Bello Mutawalle ya yi alkawarin yaki da wadannan mutane da zarar an gama yaki da ‘yan bindiga.
Jihar Zamfara dai ta kwashe sama da watanni uku a cikin wasu tsauraran matakan tsaro wadda kuma jami'an gwamnatin da su ka kira wannan taron manema labaru su ka ce matakan sun haifar da da mai-ido, duk kuwa da kokawan da al'umar jihar su ka dunga yi a wancan lokachi.
Saurari rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna a Najeriya: