Rashin samun matsaya game da bukatun jami'o'in Najeriya dai ya sa malamai komawa yajin aikin gargadi amma bayan kwashe wata guda sai kungiyar malaman Jami'o'in Najeriya wato ASUU ta sake sanar da karin watanni biyu sakamakon abin da ta kira rashin cika alkawari.
Sai dai ganin halin da dalibai ka iya shiga ya sa kungiyar iyaye da malaman makarantu kira ga bangarorin biyu cewa su sauya tunani, in ji shugaban kungiyar na Kasa Alh. Haruna Danjuma.
Ita ma kungiyar Kiristoci ta kasa CAN, reshen jihar Kaduna ta bakin Shugaban kungiyar ta CAN, Rabaren Joseph John Hayeph, ya ce lokaci ya yi da ya kamata gwamnatin tarayya ta cika alkawurran da ta yi, ita kuma kungiyar malaman Jami'o'in ta sassauta.
Yanzu haka dai daliban Jami'o'in gwamnati a Najeriya na gida sama da wata guda abun da ya sa wasu ke ganin akwai babbar matsala idan mahukunta ba su dauki matakan da su ka dace ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: