KADUNA, NIGERIA - Dalar masarar da ta kai 21 dai manoma ne da babban bankin Najeriya ya ba su bashi su ka tara ta domin bayyana nasarar da aka samu a shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noma a kasar.
Gwamnan babban bankin Najeriya, Mr. Godwin Emefele wanda Mr. Philip Yila Yusif ya wakilta ya ce wannan dalar masara ta taimaka wajen karya farashin masara a kasuwa.
Shi kuwa shugaban kungiyar manoman masara a Najeriya Alhaji Bello Abubakar Annur Funtua cewa ya yi wannan masara ma kadan ce daga abun da aka noma bana.
Sai dai ganin kusan watanni biyar da wucewar damunar da aka noma wannan masara ya sa mai sharhi akan al'amuran yau da kullun, Comared Abubakar Aliyu Umar yin wasu tambayoyi game da wannan batun.
To amma kuma gwamna Nasuru Ahmed El-rufa'i wanda kwamishinan noma, Malam Ibrahim Husaini ya wakilta ya ce wannan shiri nasara ce ga kasa baki daya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara: