Bayan wani mummunan hari da ake zargin wani jirgin sojojin Najeriya ne ya kai akan wasu fararen hula a jihar Kaduna, lamarin ya haddasa rudani da zaman zullumi.
Wani jirgin yakin rundunar sojojin Najeriya ya yi hatsari da safiyar yau Jumma'a a birnin Fatakwal.
Rundunar sojan Najeriya ta yi Allah wadai da harin tsokana da wasu masu zanga-zangar siyasa su ka kai wa kwamban motocin sintirinta a kan hanyar Lafiya zuwa Makurdi.
Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya ta yi watsi da jiya-jitar cewa babban hafsan Hafsoshin tsaron kasar, Janar CG MUSA ya mutu.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske a kan wani harin kwanton bauna da mayakan Boko Haram su ka kai a kan tawagar motocin Gwamnan Jihar Yobe.
Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Remi Tinubu ta tallafa wa matan sojojin da suka rasa mazajensu a filin daga da kuma marayun da aka bar masu da kudade.
MDD ta ce, shigar mata cikin gwagwarmayar a matakai daban daban zai taimaka wajen karfafa rundunar soji, don haka majalisar dinkin duniya za ta ci gaba da marawa Gwamnatin Najeriya a kokarinta na cike gibin da ake samu na jinsin mata a aikin soji.
Daraktan cibiyar tattara bayanan ya yi karin bayanin cewa rundunar tsaron na daukar zaben da matukar muhimmancin gaske, don haka za a yi duk abin da ya dace wajen samar da tsaro yayin zaben.
Hukumar bada agajin gaggawa ta birnin Tarayya wato- FEMA ta ce fashewar wata tankar Gas ne ta janyo gobarar da ta haddasa mutuwar mutane biyu 'yan Najeriya da kuma raunata wasu karin biyu a fishin jakadancinta da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya ta yi karin haske kan wasu tagwayen hare-hare da jiragen yakinta su ka kai kan gungun wasu yan bindiga a kan iyakokar jihohin kebbi da zamfara.
A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da karin ministoci uku da majalisar dattawan kasar ta tantance da su kwanan nan.
Rundunar tsaron kasar ta ce sun kuma cafke karin wasu ‘yan ta’adda guda dari da goma sha hudu.
Jiragen yakin Najeriya sun sami nasarar auna mabuyar ‘yan ta'addar Boko Haram a zirin tafkin Chadi, yankunan Tumbun Fulani da Tumbun Shitu inda ake ganin na zama barazana ga cibiyoyin soji da ma al'ummar yankunan.
A daidai lokacin da ‘yan awaren da ke rajin kafa kasar Biafra ke ci gaba da neman haddasa tarzoma, jiragen mayakan saman Najeriya sun kai hari a rumbunan adana makamansu a jihohin Imo da Anambra, lamarin da kwararru da mazauna yankin suka yaba da shi.
Gwamnatin jihar Zamfaran ta nemi gwamnatin Tarayya ta mata karin bayani kan zaman sulhu da yan bindiga cikin sirri da wasu jami’anta ke yi a jihar ba tare da saninta ba ko ma jami’an tsaron da ke jihar.
Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya na ta rige- rigen zuwa hedkwatar rundunar sojojin Najeriya don neman karin dauki bisa tsanantar aika-aikar 'yan bindiga dadi a yankunansu.
A wani yunkurin shawo kan kalubalen tsaro da ke fuskantar kusan kowanne bangaren Najeriya, Sufeta Janar na 'yan sandan kasar ya jagoranci wani taron tsaro da manyan jami'an rundunar daga ko'ina cikin kasar
Domin Kari