Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Yakin Rundunar Sojojin Najeriya Ya Yi Hatsari A Birnin Fatakwal


Hatsarin Jirgin Sama
Hatsarin Jirgin Sama

Wani jirgin yakin rundunar sojojin Najeriya ya yi hatsari da safiyar yau Jumma'a a birnin Fatakwal.

Hedkwatar Rundunar mayakan saman Najeriya ta ce jirgin yakin samfurin M35P ya fado ne da misalin karfe bakwai da minti arba'in da biyar na safiyar yau jim kadan bayan ya tashi da niyyar kai farmaki kan masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.

Sanarwar wacce kakakin rundunar mayakan saman Air Commodore Edward Gabkwet ya sanyawa hanu tace, baki dayan sojoji biyar dake cikin jirgin suna raye koda yake dai sun dan sami raunuka kuma a halin yanzu suna murmurewa a wani asibiti.

Tuni kuma babban hafsan hafsoishin rundunar sojojin saman Air Marshall Hassan Abubakar ya kama hanyar zuwa birnin na Fatakwal don ganewa idonsa abin da ya faru.

Kokarin da wakilinmu a Abuja ya yi don jin musabbabin wannan hatsari daga rundunar mayakan saman ya cimma ruwa, sai dai Rundunar ta ce binciken da za a kaddamar shine kadai zai bada cikakken bayani akan abin da ya janyo hatsarin.

Hatsarin jirgin yakin sojoji dai wani abu ne da ke tunatar da irin yanayin da matuka jiragen da ma sauran mayaka ke shiga a irin kokarin da a ke yi na kare Najeriya da 'yan Najeriyar.

A baya bayan nan dai jiragen yakin na ta kai hare hare akai akai ga 'yan tsirarun yankin Niger Delta da ke satar danyen mai.

Domin ko a jiya ma sai da jirgin ya afkawa 'yan tsirarun dake satar mai a Okrika da Tsibirin Bonny inda ya rugurguza wasu haramtattun matatun mai da jiragen ruwan da ake satar mai da su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG