Hari na baya bayan nan da mayakan Boko Haram suka kai garin Gaidam dake arewacin jihar Yobe, yayi sanadiyar mutuwar mutane bakwai inda mahukunta suka tabbatar da mutuwar mutane bakwai.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Yobe tace cikin mutane bakwai da suka rasu akwai maza shida da mace daya.
Bugu da kari, yan ta’addan sun kone gidaje tara da shaguna biyu da kuma motoci biyu.
Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa a jihar ta Yobe (YOSEMA) Dakta Goje Mohammed, ya shaidawa Muryar Amurka cewa tuni Gwamna Mai Mala Buni ya bada umurnin akai daikon gaggawa ga wadanda ibtila’in ya rufta da su.
Kawo yanzu Hukumar YOSEMA ta kammala kididdigar abubuwan da ya faru kuma Gwamnan Yoben ya bada umarnin kai karin kayan agaji.
Dr Mohammed ya kara da cewa bayan kayayyakin masarufi da kayayyakin shimfida, gwamnatin jihar Yoben ta bada umarnin sake Gina gidaje da majami’ar da yan ta’addan suka kona.
Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta ce yan ta’addan sun hallaka wani limamin coci da mambobinsa guda biyar.
Shugaban Kungiyar CAN reshen jihar Yobe, Fasto Yohanna Audu, ya ce farmakin da aka kai ya kuma yi sanadiyar konewar majami’a ta COCIN.
Tuni kuma malaman addinin Musulunci a jihar ta Yobe suka yi Allah wadai da wannan aika aikar da suka bayyana a matsayin ta’addanci.
Imam Abubakar Diyar, da a baya ya jagoranci shiga tsakanin Gwamnatin Tarayya da Boko Haram, ya nemi yan ta’addan da su tuba su daina wannan danyen aiki da baida alaka ta kusa ko ta nesa da addinin Islama.
A saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina
Dandalin Mu Tattauna