ABUJA, NIGERIA - A wani taron manema labaru da ya gudanar, Daraktan cibiyar samar da bayanai a hedkwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar ES Buba ya ce an kubutar da daliban ne biyo bayan wani farmaki da dakarun suka kaddamar akan yan bindigan.
Ya ce matsin lambar sojoji da ya biyo bayan farmaki akan ‘yan ta'addan ya yi tasiri da hakan ya gigita ‘yan ta'addan da ma daliban.
''Ka kwatanta yadda zaka iya kula da dalibai dari da talatin da bakwai a daidai lokacin da ake tsaka da barin wuta, mu sojoji a daidai wannan lokaci, muradinmu shine kubutar da daliban. Kuma mu kayi amfani da wannan dama muka kubutar da su.”
Janar Buba ya ce irin rudewar da daliban su kayi ya baiwa sojoji kyakkyawar yanayin kubutar da su wanda hakan ya nuna irin kwarewar dakarun.
To sai dai kuma, a gefe guda masana tsaro da tattara bayanan sirri na da tababa akan bayanan na sojojin.
Dr. Yahuza Ahmed Getso wanda ya gudanar da bincike a wannan daji ya ce bai gamsu da kalaman na sojojin ba.
A cewarsa wadannan yaran ‘yan bindigan sun tsaresu ne a tsakanin dajin Munya da dajin Koli inda anan aka tsare daliban jami'ar gwamnatin tarayya ta Gusau da ma sauran daruruwan wasu mutane da aka sace, saboda haka wace irin dabara aka yi wajen kubutar da daliban Kuriga amma aka gaza amfani da ita wajen kubutar da daliban Gusau da sauran mutanen da ake tsare da su a wannan daji.
Ganin dai a baya yawancin kubutar da mutane da sojin keyi daga ‘yan bindiga akan sami ko dai asarar rai ko jin rauni daga bangarorin biyu, amma a wannan karo ba bu wani bangaren da ya sami wata matsala. Abinda ma da ke ci gaba da sanya shakku a zukatan ‘yan Najeriya.
Koma dai menene babban abin farin cikin dai shine an kubutar da daliban salin alim.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Dandalin Mu Tattauna