A daidai lokacin da matsalolin tsaro ke kara ta'azzara a sassan Najeriya daban-daban, majalisar dattawan kasar ta gudanar da zama na musamman a jiya Talata, domin nemo bakin zaren warware matsalar.
Gwamnatin tarrayar Najeriya ta bayyana takaicinta bisa kasa cimma kudirinta na yi wa kashi biyu bisa uku na al’ummar Najeriya da suka cancanci a yi musu allurar rigakafin cutar coronavirus nau’in Astrazaneca kashi na farko.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana kaduwarsa kan yadda mayakan Boko Haram suka kai hari a garin Geidam, abin da ya kwatanta a matsayin mai matukar "ta da hankali."
Allah ya yi wa Hajiya Maryam Ado Bayero matar tsohon sarkin Kano marigayi Ado Bayero kuma mahaifiyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero rasuwa.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta sami nasarar dakile wani harin 'yan kungiyar Boko Haram, ta hanyar amfani da jiragen yaki, inda suka fatattaki mayakan a garin Geidam da ke jihar Yobe.
A yayin da hukumomin tsaro a Najeriya ke cigaba da tsare ‘yan kasuwan canji da gwal sakamakon zargin su da tallafawa ayyukan ta’adanci, yan uwa da abokan mutanen da ke tsaren na cigaba da kokawa kan rashin sanin halin da ‘yan uwan nasu ke ciki.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar da gwamnatin tarayyar kasar karkashin jagorancin shugaba Muhammadu ta gabatar mata a cikin watan Mayun shekarar 2020, na neman rancen dala biliyan biyu da miliyan 700 cikin dala biliyan biyar da miliyan 500 daga waje.
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa an gudanar da jana'izar gomman mutanen da 'yan bindiga suka hallaka, bayan wani mummunan hari da suka kai a wasu kauyuka 4 a ranar Laraba.
Hukumomin tsaron Najeriya na ci gaba da kamen mutanen da ake zargi da taimakawa ta’addanci a kasar, baya ga 'yan kasuwar canji da ke tsare a hannunsu tun kusan watai 3 da suka gabata.
Babban bankin Najeriya wato CBN ya ba wa masu fitan kayayyaki tabbacin cewa zasu cigaba da samun sahihan bayanai kan irin ribar da su ke samu a kan kayayyakin da su ke fitar da su zuwa kasashen waje ba tare da fuskanta matsaloli ba.
A yayin da hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA ta cika shekara 20 da kafuwa a Najeriya, ‘yan kasar sun fara bayyana mabambantan ra’ayoyinsu game da tasirin ayyukan hukumar a fadin kasar.
Ministan ayyukan yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, ya ayyana karshen watan Yuli a matsayin wa’adin kamala binciken kwakwaf na badakalar da ta mamaye ayyukan hukumar raya yankin Neja Delta wato NDDC.
Ana ce-ce-ku-ce dangane da sanarwar da daya daga cikin rassan jam'iyyar PDP a jihar Kano ya fitar, inda ya ce ya dakatar da tsohon gwamnan jihar Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da magoya bayansa har tsawon wata uku.
Hukumar yaki da cututtuka masu saurin yaduwa a Najeriya wato NCDC, ta bayyana cewa ana samun raguwar adadin masu kamuwa da cutar coronavirus a kasar tana mai cewa, a tsawon mako guda cutar ba ta yi kisa ba.
Gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana sabon tsarin da gwamnati ke nazari a kai, na daina baiwa masu shigo da sikari da alkama kudaden kasar waje don bunkasa kudadden ajiyar ketare.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dage haramcin saya da yin rijistar sabon layin wayar salula wato SIMCARD a turance.
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya jadada mahimmancin yin gagarumin gyara a tsarin zabe a Najeriya ya koma tsarin mayar wa masu kada kuri’u ikon da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su.
Hukumar yaki da cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce ana samun karancin karbar rigakafin cutar korona a Abuja babban birnin kasar, da kuma wasu jihohi, a shirin ba da rigakafin kashi na farko da ake cikin gudanarwa.
Kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan ayyukan kula da kiwon lafiya ya yi barazanar ba da umarnin kama magatakardan majalisar likitoci da suka hada da masu kula da hakori ta Nijeriya, Tajudeen Sanusi.
Kudurin nan mai taken ‘Dokar bada kariya da hana tsangwama da nuna banbancin addini na shekarar 2020 ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dokokin Najeriya.
Domin Kari