Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’ummar Najeriya Kaso 58.3 Ne Aka Yi wa Allurar Rigakafin Cutar COVID-19 - Gwamnati


Mista Boss Mustapha
Mista Boss Mustapha

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta bayyana takaicinta bisa kasa cimma kudirinta na yi wa kashi biyu bisa uku na al’ummar Najeriya da suka cancanci a yi musu allurar rigakafin cutar coronavirus nau’in Astrazaneca kashi na farko.

Boss Mustapha ya ce 'yan ’Najeriya miliyan 1,173, 869 kwatankwacin kaso 58 da digo 3 cikin 100 na al’ummar kasar baki daya, aka yi wa allurar, adadin da ya ce ya yi kasa bisa ga hasashen da aka yi a baya.

Haka kuma, Boss Mustapha, ya yi wa ‘yan kasar tuni kan cewa, har yanzu akwai cutar korona birus kuma ta na cigaba da illa tana kara bazuwa a wasu kasashen duniya.

Kazalika a taron, babban darakta a hukumar kula da lafiya a matakin farko, Dakta Faisal Shua’ib, ya fadi cewa ana sa ran shigo da karin wasu allurar rigakafin cutar Covid-19 a cikin watan Mayu ko Yuni na wannan shekara ta 2021 daga kungiyar COVAX dake tallafawa kasashe marasa karfi.

Daga cikin Allurar rigakafi na Astrazeneca sama da Miliyan 4 da aka shigo da su Najeriya a watan Maris dai, gwamnati ta ce ta raba su kashi biyu, kashi 50 ga wadanda aka fara yi wa sannan kashi 50 don sake yi musu a karo na biyu.

Idan ana iya tunawa, farkon shigowa da allurar, an fuskanci turjiyya sakamakon fargaba da ‘yan kasar ke nunawa kan karbar rigakafin duba da wasu kasashen turai da suka dakatar da yin amfani da nau’in na Astrazeneca saboda batun daskare jini aka alakanta da allurar.

XS
SM
MD
LG