Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Janye Tallafin Siyo Sikari Da Alkama Daga Kasashen Waje


Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana sabon tsarin da gwamnati ke nazari a kai, na daina baiwa masu shigo da sikari da alkama kudaden kasar waje don bunkasa kudadden ajiyar ketare.

Babban bankin Najeriyar ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter ya na mai cewa, Sikari da alkama za su shiga cikin jerin kayan da za a haramta shigo da su cikin kasar inda gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya bukaci ‘yan kasa su hada karfi da karfe da bankin wajen aiki domin a fara samar da kayayyakin a cikin gida maimakon shigo da su daga kasashen ketare.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2015 ne babban bankin kasar ya sanar da janye tallafin bai wa masu shigo da kayan abinci dalar Amurka, kayan da suka hada da shinkafa, da wasu kayan abinci nau’i 41.

Haka kuma, a cikin watan Agustan shekarar 2019 babban bankin ya sanar da dakatar da bai wa masu shigo da madara daga kasashen ketare dalar Amurka, inda ya ce za a iya bunkasa wadda ake da su a gida.

A wani bangare kuma, gwamnan babban bankin Najeriyar, Godwin Emefiele, ya tsoma baki kan ce-ce-ku-ce tsakanin gwamna Godwin Obaseki da ministar kudi, Zainab Ahmad kan batun buga kudade da suka kai naira biliyan 60 don cike gibi a kudaden da kwamitin rabon arzikin kasa wato FAAC, ke yi wa matakan gwamnatin tarayya zuwa kananan hukumomi wanda kwamitin ya rabawa jihohin kasar 36 hade da birnin tarayya Abuja a watan Maris.

A yayin jawabi da manema labarai a garin Awe na jihar Nasarawa, Emefiele, ya ce, bai kamata a ce ce-ce-ku-cen ya auku tsakanin mutanen biyu ba.

A karshen makon jiya ne, gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya fito da maganar da ta janyo ce-ce-ku-cen a lokacin da ya zargi gwamnatin tarayyar kasar da buga kudade tsakanin naira biliyan 50-60 domin cike gibi a kudadden da ake rarrabawa jihohin kasar.

Sai dai, ministar kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmad a karshen taron majalisar zartarwa da aka saba gudanarwa a ranar Laraba na mako-mako, ta bukaci a yi watsi da kalaman na Obaseki tana mai cewa abin takaici ne hakan ya fito daga bakin gwamna kuma babu kamshin gaskiya a cikin maganar.

Lamarin da Obaseki a martaninsa, ya kara jadada cewa, ya na nan kan bakarsa ta cewa an buga kudaden da ya ambato, yana mai bukatar gwamnatin tarayyar kasar ta daina boye-boye tare da shawartar gwamnati ta dauki matakin gaggawa don kara sake fadawa cikin komadar tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG