Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya wa'adin ranar 16 ga watan nan na Afrilu, domin karasa kashi na farko na rigakafi cutar ta COVID-19.
To sai dai rahotanni daga birnin tarayya Abuja da wasu jihohi 8, sun bayyana cewa, ‘yan kasar ba sa fitowa yadda ya kamata don su karbi rigakafin, duk da yake ana sa ran jihohin su kammala ba da kashin farko na rigakafin a ranar 16 ga watan nan da mu ke ciki saboda a fara ba kashi na biyu na rigakafin.
Wasu ‘yan kasar sun lashi takobin bijirewa karbar allurar, suna cewa "akwai matsalolin da suka addabi mutane kamar na tsaro ba rigakafi kadai ba," a cewar wasu rahotannin.
Kididdigar hukumar lafiya a matakin farko wato NPHCDA, ya yi nuni da cewa, jihohi kamar su Legas, Ekiti, Ogun, Ondo, Osun, Katsina, Yobe, Kwara, Niger, Asamawa, Gombe, Jigawa, da Kaduna, sun ba wa ‘yan kasa tsakanin kaso 60 da 111 rigakafin na korona a karon farko.
Sai dai kididdigar hukumar lafiya a matakin farko ta Najeriyar, ta nuna cewa, babban birnin tarayya Abuja, da jihohin Abia, Anambra, Akwa-Ibom, Ebonyi, Enugu, Rivers, Sokoto da Kogi, har yanzu ba su sami ba da kashi 50 cikin dari na rigakafin ba.
Haka kuma, alkaluman sun bayyana cewa, jihar Abia ta ba da kaso 14.9 ne kawai ya zuwa yanzu, jihar Akwa Ibom kashi 28, jihar Anambra kaso 22.8, jihar Ebonyi kaso 31, jihar Enugu kaso 30.1, jihar Ribas kaso 30.6, Sokoto kaso 33, Taraba kaso 19.5, a yayin da babban birnin tarayya Abuja ke da kaso 33.3 cikin 100.
Sai dai hukumar birnin tarayya Abuja ta bayyana akasin rahoton hukumar ta NPHCDA ta fitar, wanda ta ce an yi ne bisa la'akari da adadin rigakafi 228,400 da aka ba ta, tana mai ikirarin cewa, adadin rigakafin da gwamnati ta bai wa birnin Abuja ya zarta wanda ya kamata a bayar da 120,000 da ta ke bukata.
Mukadashin babban sakataren hukumar lafiya a matakin farko reshen birnin tarayya Abuja, Dakta Iwot Ndayo, ya bayyana wa manema labarai cewa, birnin Abuja ya samu nasarar bada kashi 70 cikin 100 na rigakafin, sabanin adadin da hukumar NPHCDA na gwamnatin tarayya na kaso 33.3.
A martanin ta dangane da kauracewa allurar rigakafin a jihar Abia, gwamnatin jihar ta ce ba ta sanya ranar fara ba da rigakafin gama-garin al’ummar jihar ba sakamakon fadada aikin ba da rigakafin zuwa ga karin wasu rukunin ma’aikata da ke kan gaba wajen aikin yaki da cutar ta korona.
Gwamnatin jihar Anambra ta yi ikirarin bai wa mutane dubu 22,861 rigakafin korona sabanin adadin dubu 9, ko kashi 22.8 da alkaluman gwamnatin tarayya ya nuna, kamar yadda kwamishinan lafiyar jihar, Takta Vincent Okpala, ya bayyana wa manema labarai.
Sai dai dakta Vincent bai amsa tambaya da manema labarai su ka yi masa kan alkaluman kididdigan gwamnatin tarayya kan jihar Anambra ba.
Jihar Anambra dai ta karbi rigakafin Astrazeneca 78,000 daga gwamnatin tarayyar Najeriya.
Ita ma gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta ce babu wani abin fargaba kan kason mutane da suka karbi rigakafin korona birus a jihar a halin yanzu inda kwamishinan jihar ya bayyana cewa, sun sanya ka’ida a aikin ba da rigakafin don a bi tsarin da ya kamata yana mai cewa, aikin rigakafin bai kai karo na 3 da kowa zai iya samu ba sakamakon yadda aka ba wa ma’aikatan jinya da ke kan gaba a yaki da cutar da wasu masu ruwa da tsaki mahimmanci.
Babban sakataren hukumar lafiya a matakin farko na jihar, Dakta George Ugwu, ya bayyana cewa an bai wa mazaunan jihar akalla dubu 10 rigakafin korona, adadin da ya zo daidai da wanda hukumar NPHCDA ta fitar.
A cewar Dakta George Ugwu, an sami gaggarumin kari a adadin mutane da suka nuna sha’awar karbar rigakafin, sabanin yadda aka sami karancin mutanen da ke sha’awar karba a lokacin da gwamnatin jihar ta karbi rigakafin, biyo bayan cece-kuce da fargaba kan sahihancin rigakafin.
A wani bangare kuma, gwamnatin jihar Kano ta cigaba da wayar da kan al’umma kan karbar rigakafin cutar korona inda a halin yanzu gwamnati ta bai wa mazaunan jihar rigakafi 50,931 kwatankwacin kaso 48.6 na mutanen da aka tsara ba wa.