Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dattawan APC Sun Yi Musayar Kalamai Kan Yanayin Tabarbarewar Tsaro


A daidai lokacin da matsalolin tsaro ke kara ta'azzara a sassan Najeriya daban-daban, majalisar dattawan kasar ta gudanar da zama na musamman a jiya Talata, domin nemo bakin zaren warware matsalar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ayukan 'yan ta da kayar baya musamman a jihohin Yobe da Borno da ke arewa maso gabas, Kaduna, Neja, Sokoto, Zamfara, Katsina da Kebbi da ke Arewa maso yamma, da kuma a jihohin Anambra da wasu jihohin yankin kudancin kasar.

To sai dai a lokacin zaman, an sami ta da jijiyoyin wuya tsakanin wasu 'yan majalisar biyu duka na jam'iyyar APC mai mulki, Smarts Adeyemi na jihar Kogi da Remi Tinubu ta jihar Legas, lamarin ko ya kai su ga yin musayar zafafan kalamai.

A yayin bayar da gudummawa lokacin muhawarar, Sanata Smart Adeyemi ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya dauki matakan gaggawa wajen kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Adeyemi ya ce wannan ita ce matsalar tsaro mafi muni da kasar ta taba fuskanta, wanda a cewarsa, ta ma fi ta yakin basasa ma muni.

Dan majalisar ya tuna lokacin 'yan Najreiya kan yi tafiya cikin mota daga iyakar kasa har ya zuwa karshenta ba tare da wata fargaba ba, amma kuma ya bayyana takaicin cewa a yanzu, shiga mota daga Abuja zuwa Naija ya kasance tamkar "shiga tarkon mutuwa."

Sanata Adeyemi ya kuma bayyana bacin rai akan yadda ake siyasantar da matsalar ta tsaro da ta addabi 'yan Najeriya, ta yadda "babu wanda ke iya yin bacci da ido biyu a rufe."

To sai dai alama wadannan kalaman na Sanata Adeyemi ba su yi wa Sanata Remi Tinubu dadi ba, inda ta mike ta kuma yi raddi kan kalaman na shi, tare da siffanta shi da "kura a cikin fatar akuya."

Remi, wadda ita ce matar mai dakin jigon jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ta zargi Adeyemi da kokarin shafawa jam'iyyar da ta kai shi a majalisar bakin fenti a maimakon kare martabar ta a majalisar.

Wannan dai ya kai su ga musayar kalamai masu zafi, inda shi ma dai Sanata Adeyemi, ya zargi Remi da fifita jam'iyyar APC akan "rayukan 'yan Najeriya da ke ci gaba da salwanta a kowace rana."

A hukumance dai, majalisar dattawa ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya zage damtse domin magance matsalar tsaron da kasar ke ci gaba da fama da ita.

XS
SM
MD
LG