Hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA dai ta bayyana nasarori a fanonnin kirkire-kirkiren zamani, bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi ga matasa da dai sauran ayyukan cigaba kamar yadda babban darakta, Kashifu Inuwa ya bayyana a daidai lokacin da hukumar ta cika shekara 20 da kafuwa.
Najeriya dai na kokarin shiga jerin kasashen duniya dake kan gaba a ayyukan cigaba ta fannin kirkire-kirkiren fasahar zamani wanda ke cikin manufofin da ya sa gwamnatin tarayyar kasar ta kafa ta a shekarar 2001.
Tuni dai ‘yan Najeriya ke tofa albarkacin bakin su da ma bayyana mabanbantan ra’ayoyin su game da ayyukan NITDA. Wasu sun yabawa kokarin hukumar yayin da wasu ke cewa, akwai wasu kalubalen da ya kamata a mayar da hankali a kai don magance kuma da akwai sauran jan aiki a gabanta.
Hukumar NITDA dai ta fuskanci matsalolin da ya sa wasu masu ruwa da tsaki suka bukaci a shekarun baya a rufe ta.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa hukumar NITDA ne a watan Afrilun shekarar 2001 biyo bayan amincewa da kudurin manufofin fasahar sadarwa da majalisar zartarwar kasar ta yi a watan Maris na shekarar 2001, kudurin da majalisun kasar suka zartar zuwa dokar hukumar NITDA a shekarar 2007.
Saurare cikakken rahoton a sauti: