Mazauna garin Gauraka da ke karamar hukumar Tafa a jihar Naija sun rufe titin Abuja zuwa Kaduna, a wata zanga-zanga, inda suke neman gwamnati ta kawo karshen matsalolin masu garkuwa da mutane da ayukan ‘yan bindiga a jihar da ma kasa baki daya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ayyana kwanaki uku na zaman makokin rasuwar babban hafsan sojin Najeriya da wasu manya da kananan hafsoshi da suka rasa ransu a hatsarin jirgin sama da ya auku a a karshen makon da ya gabata a Kaduna.
George Olufade mahaifin matukin jirgin saman da ya yi hatsari a Kaduna ya bukaci a rika kula da walwalar matukan jiragen saman yana mai kokawa kan cewa, dan sa ya dawo daga Maiduguri ba tare da hutawa ba aka yi tafiyar da ta yi sanadiyar mutuwarsa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta fara ba da tallafin naira triliyan 2.3 don rage radadin matsin tattalin arziki sakamakon annobar korona birus a sassan kasar daban-daban daga gobe Litinin 24 ga watan Mayu.
Hakan na nufin cewa, farashin da ake sayar da dala a kasuwanni bayan fagge za’a ci gaba da amfani da shi na naira 480 kowacce dala 1 daga yanzu.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbi fam miliyan 4.2 da aka kwato daga hannun dangin tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, wanda ya wawure kudaden al’uma kamar yadda kakakin Atoni Janar din kasar Umar Jibrilu Gwandu ya tabbatarwa da Muryar Amurka.
Akalla masallata 11 da suka hada da wani jariri da ‘yan bindiga suka yi awun gaba da su a yayin da suke tsaka da Ibadar Tahajjud sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga da suka sace su karamar hukumar Jibia.
Iyayen sauran daliban jami’ar Greenfield 20 na jihar Kaduna da suka rage a hannun ‘yan bindiga na rokon gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna da sauran masu ruwa da tsaki da su taimaka masu cikin gaggawa don ceto ’ya’yansu.
Jami’an rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara sun samu nasarar kama wasu gungun mutane da ake zargi ‘yan bindiga masu hannu dumu-dumu a ayyukan yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, satar shanu, tare da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba a cikin jihar ta Zamfara.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa, ta samu nasarar kubutar da kimanin mutum 30 daga cikin 40 da 'yan bindiga suka sace a lokacin suna ibada a Masallaci.
Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da samame a jihar Kano inda ta samu nasarar kama wasu da take zargi mambobin kungiyar Boko Haram ne a wani mataki na tsaurara matakan tsaro a dukkan sassan kasar.
Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun sauya matsayarsu a kokarinsu na samo mafita mai dorewa kan yajin aikin gama-gari sakamakon fafutukar da kungiyar ma’aikatan kungiyoyin bangaren shari’a da majalisun jihohi na Najeriya ke yi na neman a aiwatar da ‘yancin cin gashin kansu.
Rahotanni sun ce an saki daliban ne a yankin Kidanda da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, wacce ke arewa maso yammacin Najeriya da misalin karfe hudu na yammacin Laraba.
A baya-bayan nan ne jam’iyyar PDP mai adawa, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka dokar ta-baci saboda matsalolin tsaro da jam'iyyar ta ce sun yi wa kasar katutu.
Rundunar sojin Najeriya ta maida martani akan kiraye-kirayen da ake yi na cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya mika mata mulkin kasar domin ceto ta daga wargajewa.
Kamfanin jirgin saman jigilar fasinjoji na Arik ya bayyana cewa, ya kamalla shirye-shiryen komawa aikin jigilar fasinjoji daga filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja zuwa Maiduguri babban birni jihar Borno.
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya wato DSS ta gargadi ‘yan siyasa, malaman addini, da sauran ‘yan kasa a kan su kiyaye irin kalaman da za su rika yi gudun ka da su ta da rikici.
Wasu majiyoyi da dama sun ce mutanen sun kashe Muhammadu ne, gudun kada ya fallasa su, domin ya gane wasu daga cikinsu.
Ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun koka da tarin kalubalen da suka fuskanta a hannun gwamnati a yayin da aka yi bikin ranar ma'aikata ta duniya.
Kasa da mako daya da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka afkawa garin Geidam lamarin da rutsa da dubban mutane tare da sa mutane sama da dubu 6 gudun hijra, wasu ‘yan bindiga sun sake afkawa garin Kanamma, da ke shelkwatar karamar hukumar Yunusari da maraicen ranar Alhamis.
Domin Kari