Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Mutane Da Ake Zargi Mambobin Boko Haram Ne A Kano


Dakarun Najeriya.
Dakarun Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da samame a jihar Kano inda ta samu nasarar kama wasu da take zargi mambobin kungiyar Boko Haram ne a wani mataki na tsaurara matakan tsaro a dukkan sassan kasar.

Kakakin runduna ta uku ta sojin kasar a jihar Kano, Kyaftin Njoko Irabor, ne ya tabbatar da wannan nasarar a yayin zantawa da manema labarai kamar yadda rahotanni a Najeriyar ke cewa.

A cewarsa, rundunar ta kai samamen ne bayan samun bayanan sirri inda suka kama wasu da suke zargi mambobi ne a kungiyar mayakan Boko Haram da suka fara mamaye sassan kasar baya ga ayyukansu a yankunan arewa maso gabas musamman jihohin Borno da Yobe.

Kyaftin Njoko dai bai bayyana adadin mutanen da rundunar ta samu nasarar kamawa ba.

Karin bayani akan: jihar Kano, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.

"An kama mutanen ne a filin Lazio da ke Hotoro da yammacin ranar Asabar a wani gida mallakar wasu 'yan jihar Borno." Jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sai dai ya ce rundunar sojin kasar za ta yi karin bayani a cikin sanarwar da za ta fitar game da samamen da kuma mutanen da ta samu nasarar kamawa a jihar ta Kano.

Tun bayan harin da mayakan Boko Haram suka kai garuruwan Geidam, Kanamma, Mainok da ke jihohin Yobe da Borno ne aka fara yadda jita-jitar kutsen mayakan na Boko Haram a wasu jihohin arewacin Najeriya kamar Neja da Kaduna.

Lamarin da ya sa aka bukaci al’umma su hada karfi da jami’an tsaro wajen bada bayanai musamman idan suka ga mutanen da ba su yarda da su ba.

XS
SM
MD
LG