Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Kubutar Da Wasu Daga Cikin Masallata 40 Da 'Yan bindiga Suka Sace a Katsina


Wasu masallata suna sallah a Masallaci
Wasu masallata suna sallah a Masallaci

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa, ta samu nasarar kubutar da kimanin mutum 30 daga cikin 40 da 'yan bindiga suka sace a lokacin suna ibada a Masallaci.

‘Yan bindigan dai sun far wa mutanen ne cikin dare a wani masallaci da ke karamar hukumar Jibiya na jihar Katsiya a lokacin da suke aikin Ibadah inda suka yi awun gaba da kimanin mutum 40 a cewar rahotanni.

Kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito, SP Gambo Isah, Kakakin rundunar 'yan sandan na jihar Katsina, ya shaidawa manema cewa, lamarin ya faru ne da tsakar daren Litinin din nan inda yan bindiga da ba a tantance adadinsu ba dauke da kirar makamai daban-daban suka kutsa cikin sabon masallacin da ke Unguwar Kwata na karamar hukumar Jibiya inda suka yi awon gaba da masallatan.

Haka kuma, SP Gambo Isah, ya ce, a lokacin da 'yan bindigan suka afkawa masallata, sun yi ta harbin bindiga a sama don tsorata al’umman yankin tare da yi wa masallata wadanda suka fito domin yin sallar Tahajjud dirar mikiyar da yin awon gaba da su kamar yadda Channels ta ruwaito.

Motocin 'yan Sanda a Najeriya
Motocin 'yan Sanda a Najeriya

Rahotanni sun ce jami'an tsaro, 'yan kato da gora da kuma al'ummar gari wadanda suka nuna bacin ransu sun yi gangami suka bi sahun 'yan bindiganr, abin da ya ba su damar kubutar da mutane 30 cikin wadanda aka sace.

SP Gambo Isah ya kara da cewa, ya kara da cewa bayan kubutar da mutane 30 cikin kimanin 40 da yan bindigan suka sace daga farko, sun gudanar da binciken tattara bayanai inda suka yi nuni da cewa akwai sauran mutum 10 da ba a san inda suke ba.

Sai dai wasu shaidu cikin al'ummar yankin sun bayyana cewa, masallatan da kansu suka tsira ba wai 'yan sanda ba ne suka kubutar da su ba.

Majiyoyi daga karamar hukumar Jibiya dai sun yi nuni da cewa, tuni mutanen da aka kubutar suka koma hannun iyalansu kuma babu wani da aka harba ko ya ji rauni.

Daliban Kankara da aka kubutar a Katsina
Daliban Kankara da aka kubutar a Katsina

Idan ana iya tunawa, a cikin shekarar nan da muke ciki ne 'yan bindiga suka sace dalibai daga makarantun gwamnati da ke Kankara, Jangeba, Kagara, Kwalejin Noma da Kaduna da dai sauransu.

Hakan na faruwa ne yayin da rundunar sojojin Najeriya ke ba da rahoton cewa, tana samun nasara a yakin da take da 'yan fashin daji a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

XS
SM
MD
LG