Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Zaman Makokin Babban Hafsan Soji da Sauran Jami'an Da Suka Rasu A Hatsarin Jirgin Sama


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ofishinsa da ke fadarsa (Instagram/muhammadubuhari)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ofishinsa da ke fadarsa (Instagram/muhammadubuhari)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ayyana kwanaki uku na zaman makokin rasuwar babban hafsan sojin Najeriya da wasu manya da kananan hafsoshi da suka rasa ransu a hatsarin jirgin sama da ya auku a a karshen makon da ya gabata a Kaduna.

Zaman makokin da shugaban ya ayyana ya kunshi baiwa dakarun rundunar sojin kasar hutun aiki a yau Litinin, haka kuma zaman makokin zai fara aiki ne daga yau Litinin zuwa jibi Laraba.

Shugaban ya ba da umarnin a sassauta tutar kasar a dukkan gine-ginen gwamnati a fadin kasar yayin da ake ci gaba da makokin mamatan.

A ranar juma’ar da ta gabatane sojojin suka rasa rayukan su, kuma aka gudanar da janaizarsu a ranar Asabar a masallacin kasa da mujami’ar addinin kirista dake Abuja inda aka binne su a Makabartar soji da ke babban birnin tarayya Abuja.

Akwatunan gawarwakin sojojin da suka mutu (Twitter/ Nigerian Army)
Akwatunan gawarwakin sojojin da suka mutu (Twitter/ Nigerian Army)

Shida daga cikin sojojin da suka rasa rayukansu Musulmai ne, an kuma yi musu sallar jana'iza a Babban Masallacin Abuja, yayin da aka yi wa Kiristoci jana'iza a babbar mujami’ar Abuja.

Sojojin dai sun gamu da ajalinsu ne kusa da babban filin tashi da saukar jirage na Kaduna, inda suke kokarin sauka domin wani halartar wani aiki, a yayin da jirgin nasu ya fado, ya kuma kashe dukan wadanda ke ciki har su 11.

Bayan samun labarin mutuwar sojojin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwa matuka ga rasa manyan hafsoshin sojin da suka hada da, LT. Janar Ibrahim Attahiru sannan ya umarci a gudanar da bincike game da abin da ya haddasa hatsarin jirgin.

To sai dai duk da yake Buhari yana a Abuja a lokacin, amma bai halarci jana'izar marigayan ba, illa dai ya tura ministan tsaro Bashir Salihi Magashi a matsayin wakilinsa a jana'izar.

Tuni kuma da ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta, suka fara bayyana mabanbantan ra’ayoyinsu kan rashin halartar jana’izar sojojin da suka rasa ransu da shugaba Buhari da mataimakinsa suka yi.

Mutane da dama na ganin ba su kyauta ba, to amma mukarraban shugaban da mataimakinsa sun kare su da cewa, a ka'ida sai an tattara bayanan sirri a tsawon sa’o’i 48 kafin a dauki matakin halartar wani taro saboda dalilan tsaro da yanayin da kasar take ciki.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG