Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan Gwamnati A Najeriya Na Fuskantar Kalubale - Kungiyar Kwadago


Tsohon hoton wata zanga-zanga da ma'aikatan Najeriya suka yi a 2017
Tsohon hoton wata zanga-zanga da ma'aikatan Najeriya suka yi a 2017

Ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun koka da tarin kalubalen da suka fuskanta a hannun gwamnati a yayin da aka yi bikin ranar ma'aikata ta duniya.

A wannan shekara dai, kamar yadda rahotanni suka nuna, ma’aikata a Najeriya sun fuskanci kalubale da dama da suka hada da kora daga bakin aiki ba bisa ka’ida ba, fafutukar ganin gwamnati ta aiwatar da biyan albashi mafi karanci na naira dubu 30 da kuma tsadar rayuwa musamman a daidai lokacin da ake cikin matsin tattalin arziki a kasar.

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, kwamarade Ayuba Wabba, ya bayana taken da suka yi wa ranar ma’aikata ta wannan shekara a matsayin “ annobar Korona birus, talauci, rashin aikin yi tare da neman walwala ga ma’ikata a kasar.”

Baya ga korafi kan halin da ma’aikata ke cıki a Najeriya musamman ma a jihar Kaduna, Kwamared Wabba ya yi barazanar kungiyar ta su na kwadago za ta dauki mataki a kasar baki daya ta hanyar fara janye ma’aikata daga dukkannin bangarori a Najeriya.

Zanga zangar lumana da yajin aiki, na daga cikin makaman da ma'aikatan Najeriya kan yi amfani da su wajen kai kokensu ga hukumomi
Zanga zangar lumana da yajin aiki, na daga cikin makaman da ma'aikatan Najeriya kan yi amfani da su wajen kai kokensu ga hukumomi

A cewarsa bangarorin sun hadada da ma’aikatan wutan lantarki, direbobin tankokin mai, malamai da sauransu.

Ya kara da cewa, za su kwashe kwanaki biyar don su gargadi gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa da suka dace.

A nata bangare, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana gobe Litinin, 3 ga watan Mayun shekarar 2021 a matsayin hutu domin bikin ranar ma’aikata ta duniya ta bana.

Ministan Kwadagon Najeriya, Chirs Ngige
Ministan Kwadagon Najeriya, Chirs Ngige

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya fitar a madadin gwamnatin kasar, inda ya taya ma’aikatan Najeriya murna saboda shaida bikin na bana, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Aregbeshola ya kuma yaba wa ma’aikatan kan hakuri, fahimta da goyan baya da suke bayarwa wajen tafiyar da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na kai kasar zuwa ga mataki na gaba.

XS
SM
MD
LG