Kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC ta yi watsi da shirin gwamnatin Najeriya na kara haraji kan lemun kwalba wanda ake cewa carbonated drinks a turance.
Rahotanni daga jira Zamfara sun yi nuni da cewa an yi jana’izar akalla mutane 143 sakamakon munanan hare-haren da yan bindiga suka kai a ranakun Laraba da Alhamis kan kananan hukumomin Anka da Bukuyyum na jihar Zamfara.
A yayin da ake ci gaba da neman bakin zare don warware matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya, masu fada a ji sun bayyana cewa komawa kan tarbiyya ta kwarai zai taimaka wajen kawo karshen miyagun iri a kasar.
Hukumar kare hakkin masu sayayya ta Najeriya wato FCCPC ta bayyana cewa kwamitin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya ta kafa domin magance tauye hakkin mabukata da rashin adalci a masana’antar ba da rancen kudi za ta rufe sana’o’in masu ba da rance ba bisa ka’ida ba.
"Idan gwaji ya tabbatar da cewa wani na kusa da shugaba Buhari ya kamu da cutar Korona ana bukatar mutumin ya kebance kan sa har sai ya warke kuma ya sake gwajin da ya tabbatar da hakan"
Kungiyar daliban arewa masu karatun digiri na daya zuwa na uku a kasar Burtaniyya sun gudanar da zanga-zangar lumana don mika kokensu a game da yanayin tabarbarewan tsaro a arewacin kasar.
Rahotanni sun yi nuni da cewa matafiya kusan 70 ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a ranar Laraba.
Rahotanni sun yi nuni da cewa yunkurin da wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya suka yi na yin watsi da matakin shugaban kasa Muhammadu Buhari game da kudirin gyaran dokar zabe ya hadu da cikas ne sakamakon matsin lamba daga gwamnonin jihohinsu.
Matasa a shafukan sada zumunta na ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi game da matakin halaka duk dan bindigar da aka kama da laifin kashe-kashe da satar mutane domin karban kudin fansa, inda wasu ke maraba da hakan wasu kuma na kushewa.
Hukumomin Najeriya dai sun sha fadin cewa suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shawo kan matsalar ta tsaro a sassan kasar musamman a arewa maso yammaci da gabashi.
Rahotanni sun yi nuni da cewa bangarorin gwamnatin Najeriya uku sun raba naira biliyan 675 da miliyan 946 daga asusun rabon arzikin tarayyar kasar wato FAAC a watan Nuwamba.
Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ji tausayin a’umma ya kai ziyara jihohin da ake kashe-kashen mutane da ba su ji ba su gani da don nuna mu su cewa ya damu da halin da su ke ciki.
Rotimi Amaechi ya ce da kudaden da jama'a ke biya don shiga jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna, ake amfani da su domin gina layin dogo daga Legas zuwa Badun.
Shin 'Yan Majalisun Najeriya Zasu Iya Yin Watsi Da Karfin Ikon Shugaba Buhari Sakamakon Rashin Cewa Uffan A Game Da Kudirin Gyara Dokar Zabe?
Gwamnatin Najeriya ta ba da rahoton cewa sabbin mutane sama da dubu 1 ne suka kamu da cutar korona birus a rana ta biyu a jere.
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja sun yi nuni da cewa ofishin mai binciken kudi na Najeriya ya gano badakalar makudan kudadde da aka kiyasta cewa ya kai naira biliyan 8 da miliyan 500 a zaurukan majalisar dokokin kasar.
"Gwamnatin Najeriya za ta dauki matakin ne don kariya ga yan kasar kuma ba bu kamshin gaskiya kan ikirari da aka cewa shirin na gwamnatin kasar ya kasance na ramuwar gayya ne."
Rahotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewa ‘yan bindiga sun nemi sama da naira miliyan daya a matsayin haraji daga al’ummomi daban-daban a kananan hukumomin Zurmi, Kaura Namoda da Birnin Magaji a Jihar ta Zamfara.
Rahotannin sun yi nuni da cewa duk da karuwa a ribar da kamfanonin sarrafa siminti ke samu a kasar, farashin siminiti na ci gaba da hauhawa cikin watanni 18 da suka gabata, lamarin da ban mamaki duk da tabbacin da masana'antun ke yi na cewa suna kara hakaka bangaren.
Domin Kari