Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi Allah wadai da abin da ta kira "halin ko-in-kula" da ta ce gwamnatin APC mai mulki ke nunawa kan hare-haren da ’yan ta’adda suke kaiwa a wasu sassan kasar daban-daban.
A baya-bayan nan 'yan bindiga sun tsananta kai hare-hare a jihohin Sakkwato, Neja, Katsina, Kaduna, da da sauran wasu sassan Najeriya, suna kashe mutane, lamarin da ya saka al’ummomin yankunan da ke fama da rashin tsaron cikin halin fargaba kusan kullum.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar ta PDP, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce ya kamata yayi Buhari ya ziyarci jihohin da lamarin ya shafa kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ologunagba ya kara da cewa abu ne mai kyau Buhari ya kai ziyara jihohin da ibtila’in ya shafa don tabbatar da cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa, na yakar ’yan ta’adda tare da nuna cewa yana sane, kuma da jajantawa ga al’umma kan matsalar tsaro da su ke fuskanta, ba wai kawai a yi ta Allah wadi da baki ba’a kwatantawa da ziyara ba.
Kazalika, sanarwar jam’iyyar PDP ta ce rashin kai ziyara don nunawa al’umma ana tare da su, tamkar nuna gazawar gwamjnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ne karara.
"Rashin samar da mafita mai dorewa a bangaren tsaro da gwamnatin Buhari ta kasa yi ya saka matsalolin ke karar tsanani a cikin shekarun baya-bayan nan" a cewar jam’iyyar PDP.
Haka kuma PDP ta ce ’yan Najeriya na sa ran cewa abin da ya kamata gwamnatin APC ta fi mayar da hankali a kai a halin da ake cici yanzu shi ne samar da hanyar da za'a kawo karshen matsalar tsaro, ta hanyar gano wadanda ke daukar nauyin batagarin da ke addabar al’umma.
Sai dai jam’iyyar PDP din ta ce duk da cewa gwamnatin da shugaba Buhari ke jagoranta ta sanar da cewa tana aiki tukuru wajen samar da tsaron, amma ta gaza daukar matakin da ya dace.
Jam’iyyar adawa ta PDP dai na zargin APC da son mulki kawai ba tare da shiryawa yin jagirancin l’umma yadda ya kamaşa ba ta hanyoyin fidda tsare-tsaren da zasu amfane al’umma.
To sai dai kuma kakakin fadar shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya musanta zargin na PDP, inda ya ce gwamnatin shugaba Buhari na iya kokarinta wajen yaki da matsalar tsaro.
Garba shehu ya ce "abubuwan da ke faruwa a game da tsaro ba bu dadi kuma ba bu wanda zai so ya ji ko ya fuskanci munanan hare-haren da yan bindiga ke kai wa kan al'umma."
Ya kara da cewa saboda haka ne ya sa gwamnatin tarayya ta tura wakilai zuwa Sakkwato da Katsina, don tattauna da wadanda al'amarin ya shafa da jami'an tsaro domin neman mafita mai dorewa.