A halin yanzu dai ana ci gaba da neman karin gawarwaki mutane sama da 100 kamar yadda wani ganau da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida mana inda ya ce mutane sama da 200 sun rasa ransa a sakamakon harin.
Rahotannin sun yi nuni da cewa ‘yan ta’addan da ke tserewa sakamakon luguden wutan jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya wanda ya raba su da matsugunin su a dajin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi, sun yi tattaki zuwa kudancin Zamfara, inda suka afka wa mutanen yankin suka kashe da dama daga ciki kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wata majiya daga yankin ta shaida cewa ana ci gaba da aikin zakulo wasu gawarwaki daga cikin dazuzzuka.
Majiyar ta kara da cewa yan bindigar sun afkawa mazaunan kauyukan kananan hukumomin Anka da Bukuyyum bayar wasu a cikin gonaki wası kuma a cikin gidajensu dikin ba’a zata.
Haka kuma, rahotanni sun yi nuni da cewa yan bindigar sun kona gawarwakin wasu daga cikin wadanda al’amarin ya shafa baya fille musu kawunansu inda ba’a iya gane su ma.
A cewar wata majiya, yan bindigar sun kai hare-haren ne ba tare da bari ko tausayawa mata da kananan yara ba inda suka yi ta cinnawa gidajen mutane wuta kuma da zarar mutane citi har da kananan yara da mata suka yi kokain tserewa suna bindige su da kona gawarwakinsu.
A halin yanzu dai mutanen da suka sami nasarar tserewa suna samun mafaka a wasu al'ummomin da suka fi samin tsaro a yanzu.
Rahotanni sun kuma yi nuni da cewa al’ummomin da yan bindigar suka afkawa sun haura 10 kuma miyagun na tafiya daga wannan al’umma zuwa waccan a kan babura suna aikata kisan gilla ga al’ummomin da ba su ji ba su gani ba.
A yayin rubuta wannan labari dai rahotanni sun yi nuni da cewa yan bindigar sun janye amma ba su yi nisa da kauyukan da aka kai farmakin ba.
An Kubutar Da Mutum Kusan 100 A Arewacin Najeriya
Baya ga kisan gilla, wata majiya ta ce kimanin shanu da sauran dabbobin gida dubu 2 ne yan bindigar suka sace yayin da kuma kona gidaje da dama da shagunan abinci.
Kazalika, majiyar ta ce yan bindigar sun kai hare-haren ne a kauyuka biyar da suka hada da Kurfa Danya, Kurfa Magaji Rafin Gero, Tungar Isa da Barayar Zaki a kananan hukumomin Anka da Bukuyyum cikin sa’ao’i 48 ba bu kakkautawa.
Rundunar sojin saman Najeriya ta aike wani jirgin yaki zuwa yankin a kokarin gudanar da aikin ceto wanda aka ce hakan bai iya cimma nasarar da ake sa rai ba sakamakon yadda 'yan ta'addar sun kutsa cikin fararen hula inda suka yi amfani da mutane a matsayin mafaka don gudun harin rundunar sojan in ji wata majiya daga Zamfara.
Har yanzu dai duk kokain ji ta bakin gwamnatin jihar da jami'an tsaro ya yi tura a yayin hada wannan rahoto.