Karamin ministan lafiya na najeriya, Dakta Olorunnimbe Mamora, ya bayyana cewa shirin gwamnatin Najeriya na sanya kasashen da suka sanya kasar a cikin jerin kasashen da ba za su shiga kasashensu ba sakamakon nau’in korona wato Omicron ba ramuwar gayya ba ne.
Mamora ya bayyyana hakan ne a matsayin karin haske kan kalaman ministan sufuri, Hadi Sirika, da ya ke cewa Najeriya za ta haramtawa 'yan Burtaniya da wasu kasahe da suka sanya ta cikin jerin kasashen red list shigowa, a yayin da ya ke magana a labaran gidan talabijan na Channels.
Dakta Mamora ya kara da cewa gwamnatin Najeriya za ta dauki matakin ne don kariya ga yan kasar kuma ba bu kamshin gaskiya kan ikirari da aka cewa shirin na gwamnatin kasar na ramuwar gayya ne.
Mamora ya ce "kar a dubi lamarin a matsayin matakin ramuwa, illa kare yan kasa. Ta fuskar diflomasiyyar kasa-da-kasa akwai abin da ake kira ka’idar yin mu’amala da juna a cikin yanayin adalci da daidaituwa."
Sai dai Mamora ya ce abu mafi mahimmanci shi ne, a matsayin Najeriya na kasa mai cikakken iko tana da ‘yancin sanin abin da ya fi dacewa da ita ta fuskar daukar matakan kare kan ta daga abubuwan da ba su dace ba, ya na mai cewa duk hanyar da gwamnati ta bi don aiwatar da hakan, ya dace da matakin da ta ɗauka don bukatun kasar.
Kazalika, ministan ya kuma yi magana game da ficewar likitocin da dama daga kasar don neman rayuwa mai inganci a kasashen waje, yana mai cewa ma’aikatan kiwon lafiya suna la’akari da yawan albashi, yanayi mai kyau, kayan aikin da ake da su, da dai sauransu kafin su bar Najeriya zuwa waje.
Sai dai Mamora ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na hada gwiwa da hukumomin da abin ya shafa domin magance matsalolin da ke tilastawa likitoci da ma’aikatan jinya barin kasar.
A cewarsa, ko me gwamnati za ta yi a kokarin inganta rayuwa, sai an sami mutanen da za su so barin kasa don kashin kansu kuma ba abinda gwamnati za ta iya yi don hana su.
Idan ana iya tunawa, alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa dubban likitocin Najeriya sun bar kasar zuwa kasashen waje don neman albashi mafi tsoka da yanayin kula da ma’aikatan jinya a kasashen da suka ci gaba.