Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ayyukan sufurin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna na samar da kudadden shiga akalla naira miliyan dari uku ga gwamnatin Najeriya a ko wane wata.
Amaechi ya ce yanzu haka da kudaden ne ake amfani wajen tafiyar da layin dogo na Legas Zuwa Badun.
Amaechi ya bayyana hakan ne a shirin Hard Copy na gidan talabijan na Channels, inda ya ce ma’aikatarsa ta fara ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Amaechi ya kara da cewa, a halin yanzu ma’aikatarsa na biyan sama da naira miliyan 100 zuwa ga lalitar gwamnatin tarayyar kasar.
Amaechi wanda tsohon gwamnan jihar Ribas ne, ya kara da cewa gwamnati na shirin sanya jiragen kasa kusan 16 don jigilar fasinjoji a kan layin dogo daga Legas zuwa Badun, yana mai jaddada cewa hakan zai kara samar da kudaden shiga daga fannin sufurin jiragen kasa.
Haka kuma Amaechi ya ce Najeriya na da karfin iya biyan bashin da ta dauka don gina layin dogon da tafiyar da shi duk da cewa masana tattalin arziki na ganin basussukan gina layin dogon ya yi yawa.
A farkon wannan shekarar, Amaechi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta karbo rancen kudi kusan dala biliyan 2.5 domin shimfida titin jirgin kasa da ya hada Legas zuwa Badun.
Amaechi ya kuma bayyana cewa ana samun karin ci gaba a fannin sufurin jiragen kasa wanda zai kara habaka samun kudaden shiga ga ma’aikatar tare da taimakawa gwamnati wajen biyan basussukan da ake bin ta.
Tuni dai 'yan Najeriya suka nuna damuwa a game da karbo basussuka masu sharudda da ke ci gaba da jefa 'yan kasar cikin matsanancin hali, inda wasu ke danganta basussuka ga sharudan IMF na kar Najeriya ta daidaita kudin dala a kasar.
Wasu kuma suna nuna fargaba a kan labarin yadda gwamnatin kasar Sin za ta karbe ikon gudanar da ayyukan filin tashi da sukan jiragen saman kasa-da-kasa daya tilo da kasar Uganda ke da shi sakamakon basussukan da ta ciwo daga kasar Sin din, suna cewa kar dai garin neman basussuka Najeriya ta saryantar da 'yancin ta na kasa mai cikakken iko da kan ta.
Kassim Garba Kurfi da ke zama masanin tattalin arziki ya bukaci gwamnatin Najeriya ta sake daura damarar samar da hanyoyin bunkasa tattalin arziki a cikin gida, ta kuma daina ciwo bashi daga kasashen waje.