A cewar hukumar lafiya ta duniya, jinin da ya ke lafiya ba tare da ya hau ba, shi ne wanda yake mizanin milimita 120 da 80 ko kasa da haka na ma’aunin mercury. Mutun ya na samun hawan jini ne idan mizanin milimita na jinin ya tsaya a 140 da 90 ko ma fiye da haka na ma’aunin mercury.
Wata girgizar kasa mai karfi ta afku a gabashin kasar Japan a yammacin ranar Juma’a, kamar yadda kafar yada labarai ta NHK ta bayyana.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta ce tana gudanar da bincike kan Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, kan zargin badakalar Naira biliyan N70B.
Dakarun sojin Najeriya sun kashe mutane sama da 70 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a wani farmaki da suka kai a yankin Arewa maso Gabashin kasar.
Dan wasan Najeriya Victor Osimhen ya zura kwallo a raga yayin da kungiyar Napoli ta lashe Seria-A ta farko cikin shekaru 33 bayan ta tashi 1-1 da kungiyar Udinese da daren ranar Alhamis.
Masu Sharhi sun bayyana damuwa dangane da makomar bakin da suka makale a Sudan sakamakon yadda aka fara zargin wasu bakin da zama sojan hayar da ke kama wa bangaren ‘yan tawaye.
Matsalar rashin tsaro na sake waiwayo wasu yankunan arewa maso yammacin Najeriya duk da yake a baya an dan fara samun sauki.
Kungiyar Young Africans ta Tanzania ta fitar da zakarun Najeriya, 'yan kungiyar Rivers United daga gasar CAF Confederation Cup.
Tinubu ya bayyana haka ne a gidansa da ke unguwar Asokoro a Abuja jim kadan bayan dawowarsa daga kasar Faransa.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli Akan Al'amuran Musulunci, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.
Gabanin zaben cike gurbi da za a yi a gobe Asabar a rumfuna 2,660 a fadin Najeriya, Sufeto Janar na yan sandan, Usman Baba Alkali ya ba wa masu kada kuri’a tabbacin kare lafiyarsu a rumfunan zabe.
Rundunar sojin Sudan ta yi gargadi a jiya Alhamis kan yiwuwar barkewar arangama da dakarun sa kai na kasar masu karfi, wadanda ta ce an girke su tura a Khartuom, babban birnin kasar da sauran wasu yankun ba tare da amincewar sojoji ba.
Mutane biyu ne suka mutu yayin da sama da miliyan guda suka rasa wutar lantarki a ranar Alhamis, bayan da dusar kankara ta afka wa larduna biyu mafi yawan jama’a a kasar Canada, gabanin hutun karshen mako.
Malaman Islama da addinin Kiristan nan biyu wato Imam Nuraini Ashafa da Pastor James Wuye sun nuna cewa hadin kan jama’a ta hanyar kauce wa bambance-bambance ne zai dawo da Najeriya kan turba mai kyau ta zaman lafiya.
Domin Kari