WASHINGTON D.C. —
Shirin na wannan makon, zai kawo muku kashi na uku na ci gaba da tattaunawa da shugabannin kungiyoyin manoma mata da maza a Najeriya wanda suka koka cewa tsohuwar gwamnatin Buhari ta ba da umarnin a basu tallafi domin su yi noma har su ciyar da kasa sannan a sayar wa wasu kasashen duniya, amma tallafin bai kai gare su ba.
Sai dai sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya ce zai ci gaba da samarwa manoma tallafi da dabarun inganta noma, domin kasar ta yi dogaro da kanta.
Saurari shirin cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna