‘Yan wasan Dutch sun doke Portugal da ci 3-2 shekara daya da ta wuce a gasar ci kofin nahiyar Turai a matakin rukuni, amma a wannan karon bangaren na Iberian ba su taka leda sosai ba a karawarsu da Netherlands da aka san ta da riga launin lemo kuma ba ta samu damar kai hari ba har sai minti na 82.
‘Yan wasan Dutch sun zura kwallo a daidai minti 13 daga bugun kwana, lokacin da Van der Gragt ta zura kwallo da kai a raga, amma mai taimakawa alkali ta daga tuta kan satar gida yayin da take tunanin Jill Roord ta yiwa mai tsaron raga tsaiko.
Sai dai an sauya hukuncin satar gida da aka yanke na yin katsalandan a wasan, bayan bitar VAR da alkaliyar wasan ta yi bayan ta sake kallon na’urar kuma ta bayar da kwallon, lamarin da ya haifar da murna ta biyu daga ‘yan wasan Dutch.
Van der Gragt ta shaidawa manema labarai bayan da aka bayyanata ‘yar wasan da tafi taka leda a wasan cewa “mun yi murnar zura kwallo a raga sannan kuma mataimakiyar alkaliyar ta daga tuta, don haka muka jira hukunci na karshe.”
“Ko yaushe yana da wahala ka yi murna karo na biyu amma yana da kyau. Na yi farin ciki sosai da muka yi nasara, wannan shi ne abu mafi muhimmanci a yau.”
Reuters
Dandalin Mu Tattauna