Fatar da ‘yan Najeriya ke da ita ta magance matsalar rashin tsaro a karkashin sabbin gwamnatoci, na ci gaba da dushewa saboda yadda ‘yan bindiga ke zafafa kai hare-hare daidai lokacin da sabbin gwamnatoci ke kusa da cika kwana arba'in kan mulki.
‘Kasa da sa’o’I 24, tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani dangane da sammacin da hukumar yaki da rashawa da kula da korafin jama’a ta jihar ta ce ta aika masa ya bayyana a gabanta domin bada bahasi kan bidiyon da ake zargi ya nuna yana karbar cin hancin daloli
Masu sharhi akan sha’anin tsaro sun hango cewa kungiyoyin ta’addancin Arewacin Mali sun fara yunkurin kafa reshe a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya inda bayanai ke nunin yadda suke sajewa da jama’a su na ratsa wasu jihohin Jamhuriyar Nijar don shiga Najeriya cikin ruwan sanyi.
Majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta ce akwai abin dubawa dangane da batun jinginar da filayen manyan tashoshin jiragen saman Najeriya da zarar an kafa kwamitin kula da harkokin sufurn jiragen sama.
An fuskanci wani yanayin zafi da ba a taba samun irin sa ba cikin shekaru a kasashen duniya a ranar Talata wanda ranar Laraba na iya zama rana ta uku a jere da za a yi fama da wannan zafi da ya kafa tarihi a duniya.
Ma'aikatar raya babban birnin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa an sami barkewar annobar cutar sarkewar numfashi na yara wato DIPHTHERIA a wasu yankunan birnin.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu a karon farko ya yi ganawar keke da keke da sabbin manyan hafsoshin kasar bayan nadinsu makonni biyu da suka shige.
Shahararriyar mawakiyar ta bayyana hake a shafinta na sada zumunta inda ta ce tana kaunar fitaccen mawakin Rema.
Gwamnatin jihar Taraba ta ayyana dokar ta baci a karamar hukumar Karim Lamido sakamakon wani rikicin kabilanci da ya yi sanadin kashe akalla mutane biyu da kuma yin kone-kone a kauyuka fiye da bakwai da suka haddasa asarar dukiyoyi.
A Najeriya, talauci shi ne babban dalilin da ke sa yara da dama ba sa zuwa makaranta, sai dai ana kara kokarin ganin an magance wannan matsala, yadda Musulmai suka gudanar da Idin babbar Sallah, da kuma wasu rahotanni
A kasar Kamaru hankalin mutane ya karkata kan matsalar da ta shafi hamshakin attajiri Alhaji Baba Danfullo, inda gwamnatin Afirka ta Kudu ta kwace kadarorinsa da dama.
Domin Kari