Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda ‘Yan Ta’addan Mali Ke Yunkurin Kafa Reshe A Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya


Yan bindiga 
Yan bindiga 

Masu sharhi akan sha’anin tsaro sun hango cewa kungiyoyin ta’addancin Arewacin Mali sun fara yunkurin kafa reshe a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya inda bayanai ke nunin yadda suke sajewa da jama’a su na ratsa wasu jihohin Jamhuriyar Nijar don shiga Najeriya cikin ruwan sanyi.

NIAMEY, NIGER - A wata hirar ta musamman da mai fashin baki kan al’amuran tsaro Abdourahaman Alkassoum ya gargadi gwamnatocin kasashen Yammacin Afrika da su dubi wannan lamari da idon basira don murkushe abinda ya kira babbar barazana.

Abdourahaman Alkassoum ya ce ana iya cewa kasar Mali da riga ta tsunduma akan yadda ‘yan ta’addan suka samu wurin zama sosai suka mamaye ta, kamar yadda Kungiyar IS ita kuma a yankin Sahel ta mamaye bakin iyaka uku na tsakanin kasashen Nijar, Burkina Faso da Malin.

Ya ce kokarin da suke yi yanzu shine na shiga sauran kasashen kewaye salim-alim.

Saurari cikakkiyar hirar su da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma:

Yadda ‘Yan Ta’addan Mali Ke Yunkurin Kafa Rushe A Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG